Kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ya ruwaito jiya Laraba cewa, bangaren Amurka ya mayar wa bangaren Sin wasu kayayyakin tarihi har guda 38, da suka bata daga Sin.
An gudanar da bikin mika kayan tarihin ne a birnin New York na Amurka da yammacin jiya Laraba, a karamin ofishin jakadancin Sin dake birnin New York. Ofishin masu gabatar da kara na kotun Manhattan dake birnin na New York ne ya mika kayayyakin tarihin da suka bace ga gwamnatin Sin.
Kasashen Sin da Amurka, sun sa hannu kan yarjejeniyar fahimta tsakanin gwamnatocin biyu, game da hana kayayyakin tarihin Sin shiga Amurka ta barauniyar hany. Karo na farko a ranar 14 ga watan Janairun shekarar 2009, kuma daga bisani aka kara wa’adin aikin yarjejeniyar a karo na uku, daga ranar 14 ga watan Janairun shekarar bana. (Safiyah Ma)