Zaunannen wakilin Sin a MDD Zhang Jun, ya yi kira ga al’ummar kasa da kasa da ta goyi bayan kasashen yankin manyan tabkuna wajen gina makoma ta bai daya.
Zhang Jun ya bayyana haka ne yayin jawabin da ya gabatar a taron da kwamitin sulhu na MDD ya shirya a fili, kan batun yankin manyan tabkuna, a jiya Laraba.
A cewarsa, a bana ake cika shekaru goma da kulla “ka’idojin kawo zaman lafiya da tsaro da kuma hadin gwiwa tsakanin kasar Kongo (Kinshasa) da kasashen yankin manyan tabkuna”, don haka kamata ya yi al’ummar kasa da kasa ta goyi bayan kokarin da aka yi na warware batutuwan Afirka bisa dabarun masu dacewa da nahiyar.
Zhang Jun ya kara da cewa, Sin ta dade da tsayawa tsayin daka kan goyon bayan neman ci gaba mai dorewa a yankin manyan tabkuna.
Ya ce “Shawarar neman bunkasuwar duniya baki daya” da kasar Sin ta fitar, ta fi mai da hankali kan kasashe masu tasowa kamar kasashen Afirka.
Har ila yau, ya ce bangaren Sin yana sa ran karfafa hadin gwiwa tsakaninsa da kasashen dake yankin bisa “Shawarar neman bunkasuwar duniya baki daya”, ta yadda za a iya zuba sabon kuzari ga kokarin neman ci gaba cikin lumana a yankin. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp