Zaunannen mataimakin wakilin Sin a MDD Dai Bing, ya bayyana jiya Laraba cewa, bangaren Sin ya sake kira ga bangarorin dake rikici da juna a kasar Sudan, da su kawo karshen tashin hankali, su inganta matakan kwantar da hankali a kasar, ta yadda za a kai ga dakile fadadar rikicin da kaucewa aukuwar munanan bala’u da barna.
Yayin bude zaman kwamitin tsaron MDD game da rikicin na Sudan, Dai Bing ya bayyana cewa, tun daga makon da ya gabata, rundunar ko ta kwana ta RSF, ta kaddamar da manyan hare-hare a El Fasher, wanda ya haddasa rasuwa da jikkatar fararen hula masu yawa, yayin da wasu suka rasa gidajensu, wanda hakan ya kara ta’azzara rikicin jin kai na Sudan.
Ya ce bangaren Sin na jaddada kira ga bangarorin da abun ya shafa, da su aiwatar da ajandar kwamitin sulhu a zahiri, kuma su daina kaiwa juna hare-hare a El Fasher.
Dai Bing ya jadadda cewa, bangaren Sin na goyon bayan dukkan kokarin diflomassiya dake himmatuwa ga inganta yanayi a Sudan, ya maido da zaman lafiya a kasar, kana yana goyon bayan MDD, da kungiyar AU, da yankuna da kasashen dake ba da muhimmiyar gudummawa ga tattaunawa, yana mai kira ga kasashen da ke da tasiri kan bangarorin biyu masu rikici da juna, da su nemi bangarorin biyu su sake komawa tattaunawa, don neman mafitar siyasa ta gaggawa ta tsagaita bude wuta na dogon lokaci.
Jami’in ya ce bangaren Sin na fatan bangarori daban daban za su himmatu, wajen mutunta ikon mallaka, da ’yancin kai, da kuma martabar cikakkun yankunan kasar ta Sudan, tare da ba da gudummawa ga dakatar da yaki, da saukaka matsalolin jin kai, da wanzuwar zaman lafiya a yankin. (Safiyah Ma)