Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU), ta zargi Babban Bankin Duniya da kuma Hukumar Bayar da Lamuni ta Duniya (IMF) da yin zagon kasa, don lalata tsarin ilimin al’umma a Nijeriya.
Kungiyar ta kuma koka a kan jinkirin da aka samu wajen sake tattaunawa da gwamnatin tarayya a shekarar 2009, inda ta ce duk da cewa, an cimma yarjejeniya da gwamnatin tarayyar da dama, amma har yanzu ba a kammala tattaunawar da kungiyar ta ASUU da kuma gwamnatin ba.
- Sin Ta Kafa Tsarin Ilimin Koyar Da Sana’o’i Mafi Girma A Duniya
- Cire Tallafin Man Fetur Ya Kawo Ƙarshen Fasa-ƙwauri, in ji NSA
Shuugaban na ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ne ya bayyana hakan ranar Talata a Abuja; yayin bikin ranar jaruman kungiyar ta 2024 zuwa 2025.
Har ila yau, shugaban ya yi nadamar bayyana yadda lamarin ya kara dagulewa sakamakon aiwatar da tsarin da aka cimma na IPPIS a jami’o’in gwamnati, bayan da majalisar zartarwa ta tarayya ta bayyana shirin cire tsarin daga makarantun gaba da sakandire.
Osodeke ya kuma nuna damuwarsa, kan yadda har yanzu gwamnatin tarayya ke ci gaba da rike wa kungiyar albashi na wata uku da rabi; ba bisa ka’ida ba, baya ga wasu bashisshikan albashin da na karin girma da kuma alawus-alawus, wanda har yanzu ba ta biya ba.
Da yake yin karin haske a wajen taron, inda kungiyar ASUU ta ta karrama wadanda ta bayyana a matsayin “Tsoffin jarumanta wadanda har yanzu ke raye”, Osodeke ya yaba wa ‘ya’yan kungiyar na kasa baki-daya, bisa “Jajircewa da sadaukar da kai da suka yi wajen wajen tabbatar da wannan kungiya tamu, wanda ke da nasaba da ‘yantar da al’ummar Nijeriya har abada.”
Har wa yau, ya kuma bayyana cewa; kungiyar za ta bayar da tallafin karo karatu na digirin-digirgir (Ph.D) ga wasu mambobinta a jami’o’in gwamnati daban-daban na wannan kasa. Tallafin, zai kasance na Naira 500,000 ga duk wanda ya yi katarin samu, sannan za a bayar da shi ne bisa la’akari da shawarwarin da kwararru daga cikin mambobin suka bayar.
“’Yan’uwa, kamar a baya ma; bikin na bana na jaruman namu na gudana ne a daidai lokacin da muke ci gaba da fafutukar ganin an ceto jami’o’in gwamnatin Nijeriya daga halin kunci, wanda Babban Bankin Duniya (World Bank) da Hukumar Bayar da Lamuni ta Duniya (IMF) suka jefa su, wadanda yunkurinsu na ruguzawa ko binne tsarin jami’o’in bai yi nasara ba.
Wadanda aka karrama a wajen taron su ne; Farfesa T. Uzodinma Nwala; Farfesa Bright Ekuerhare; Farfesa Oye Oyediran; Mallam Bashir Kurfi; Farfesa The Name Ikiddeh; Mista S.A. Fadipe da kuma Farfesa Sola Olukunle.
Sauran sun hada da; Nasir Hussain; Tunde Oduleye; Farfesa Rasheed Abubakar; Akin Oyebode; Mustapha A. Danesi; A.T. Wins; and da kuma Peter Ozo-son.