Bankikin Raya Afirika (AfDB) da Ofishin Kula da Basukan Nijeriya (DMO) sun bayyana cewa a halin yanzu suna tattaunawa tare da neman hanyar da za a fuskanci matsalolin basukan da ya addabi Nijeriya da wasu kasashen Afirika ta hanyar samar da kwararru da za su fitar da hanyoyin da za a fita daga kangin bashin.
Basukan da ke kan kasashen Afirika da dama ya kai matsayin da zai tayar da hankula wanda hakan kuma yake dora nauyi a kan kasafin kudin kasashen yana kuma dakile ayyukan raya kasa da kasashen suka shiya yi wa al’umma.
- Yadda Muka Yi Da ‘Yan Bindigar Da Suka Sace Iyalina – Sarkin Kagarko
- An Yi Taron Harkokin Waje Na Kwamitin Kolin Jam’iyyar Kwaminis Ta Kasar Sin
Binciken da babban bankin ya gudanar ya nuna cewa, a shekarar 2022 kasashen Afirka 23 sun shiga mummunan matsayi a kan tulin bashin da ya yi musu katutu. Haka kuma cikin kasashe 9 da bashi ya fi yi musu katutu a duniya 8 daga cikin su suna a yankin Afirka ne, haka kuma a cikin kasashe 27 da suke cikin wadanda ba za a iya bashi ba saboda yadda ta yi musu katutu 13 na a yankin Afirka ne, kamar yadda rahoton ya nuna.
Domin maganin wannan matsalar, Bankin Raya Afirka ya fito da tsarin samar da kwararru don su samar da mafita a kan wannan matsalar bashin da ta addabi kasa.
Sanarwar da ta fito daga bankin ta bayyana cewa, babban darakta mai kula da tsare-tsare, Eric Ogunleye, shi ne zai jagoranci shirin, tuni kuma ya nemi hadin kan kasashen Afirka domin cimma wannan manufar, ya ce, yadda kasahen Afirka ke cin bashi ba zai haifar wa da kasashen da mai ido ba.
A jawabinsa a taron da Bankin ta yi a Abuja, Ogunleye ya ce, kwamitin kwararun za su jagoranci fadakarwa da tattauna yadda za a shawo kan basukan da suka addabi kasashen Afirka tare da samar da hanyoyin kawo karshen hauhawar basukan gaba daya.