Bankuna a ranar Asabar sun ci gaba da karbar tsohuwar N500 da N1,000, a madadin Babban Bankin Najeriya (CBN), tare da yin alkawarin cewa za a ci gaba da karbar kudaden a yau Lahadi, saboda wasu ‘yan Nijeriyar na cikin damuwa kan rashin tabbas na ci gaba da karbar tsofaffin kudaden domin yin mu’amala da su.
Ziyarar da LEADERSHIP ta kai bankunan ranar Lahadi wasu bankuna da ke Legas, ya nuna cewa, sakon da aka aika wa kwastomomi a ranar Juma’a, an bude bankunan ne kawai ga kwastomomin da ke son ajiye tsohon takardunsu. Bincike ya nuna cewa suna zuwa ne kawai saboda kwastomomin da suka cika fom ta yanar gizon CBN.
- Zanga-Zangar Sauyin Kudi Ta Yi Sanadin Asarar Dukiyoyin Jama’a Da Dama A Jihar Ribas
- Me Zai Biyo Bayan Canza Wasu Kudade A Nijeriya?
A ranar Larabar da ta gabata ne babban bankin kasar CBN ya bude wa ‘yan Nijeriya da ke da tsofaffin takardun kudi na N500 da N1,000 kofar shigar da tsaffin kudadenau ta yanar gizo bayan da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa tsohuwar N200 ce kadai za a ci gaba da karba har zuwa ranar 10 ga Afrilu, 2023.
Ya zuwa ranar Juma’a, dubban kwastomomi sun mamaye ofisoshin babban bankin kasar na CBN, saboda rahotanni masu cin karo da juna na dangane da tsofaffin takardun kudi. Tun da fari dai, bankunan sun aika wa kwastomominsu sakon cewa za su karbi kudi har N500,000 daga cikin tsofaffin takardun N500 da N1,000 tare da karbar takardun daga kwastomomin da suka riga suka samar da lambobin daga shafin yanar gizon CBN.
Sai dai kuma da yammacin ranar Juma’a, babban bankin na CBN, a wata sanarwa da daraktan harkokin sadarwa na kamfanoni, Osita Nwanisobi, ya fitar, ya musanta cewa CBN ta bai wa bankunan izinin karbar tsofaffin takardun kudi.
Ya zuwa yammacin ranar Asabar, LEADERSHIP ta tabbatar da cewa bankin First Bank, Guaranty Trust Bank (GTBank), Fidelity Bank da Lotus Bank, suna karbar tsofaffin takardun daga hannun abokan huldarsu da suka cika fom ta yanar gizo tun da farko kuma suka samar da lambobin ajiyar.
An fada wa abokan huldar bankunan da ba su halarta ba da su dawo ranar Lahadi saboda za a bude bankin tsakanin karfe 10 na safe zuwa 2 na rana.