Hukumar Tsaro ta cikin gida (Civil Defence, Gandirob , Kashe Gobara da Hukumar Kula da Shige da Fice (CDCFISB)) ta amince da karin girma ga jami’ai 17,331.
Sakataren CDCFIB, Ja’afaru Ahmed ne ya bayyana karin girma ga manyan jami’an gudanarwar a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, wanda ya bayyana cewa adadin sunayen da aka fitar na karin girma ne na shekarar 2022.
A takaice, daga cikin jami’ai 17,331 da suka samu karin girma, 8,365 a Hukumar Kula da gidan gyara hali (NCoS), 3,472 a Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), 327 a Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya (FFS) sai 5,167 a Hukumar tsaron farin kaya ta Nijeriya (NSCDC).
A cewar sanarwar, Ministan harkokin cikin gida kuma shugaban hukumar, Ogbeni Rauf Aregbesola, ya bayyana karin girman ga jami’an a matsayin wata kyauta ta bankwana da gwamnatin mai barin gado, ya kara da cewa an amince da karin girman ne bisa la’akari da cancantar jami’an.