Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, tare da tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, sun isa garin Madina a ƙasar Saudiyya don halartar jana’izar fitaccen ɗan kasuwa kuma mai taimakon al’umma, Alhaji Aminu Dantata.
Mai bai wa Sanata Barau shawara kan harkokin yaɗa labarai, Ismail Mudashir, ya ce sun sauka a Filin Jirgin Sama na Yarima Mohammad Bin Abdulaziz da ke Madina da ƙarfe 5:15 na safe agogon Saudiyya a ranar Talata.
- Faɗuwar Darajar Naira Ta Sa Bashin Nijeriya Ya Ƙaru Zuwa Naira Tiriliyan 149
- Haɗakar Jam’iyyun Adawa Ba Ya Ɗaga Mana Hankali – Sabon Shugaban APC
Za a yi jana’izar Alhaji Aminu Dantata a ranar Talata a birnin Madina.
Sauran da suka raka su sun haɗa da shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas; Sanata Muntari Dandutse, shugaban kwamitin Majalisar Dattawa kan cibiyoyin ilimi da TETFund; da kuma Mataimakin shugaban marasa rinjaye na Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Ali Madaki.
Hakazalika, akwai Hon. Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari, ɗan majalisar wakilai daga yankin Makoda/Dambatta na Jihar Kano; Ahmad Munzali Dantata, ɗan marigayi Alhaji Aminu Dantata; Usman Yahaya Kansila; da Hon. Sani Bala, tare da wasu.
Dukkaninsu sun je ne domin girmama marigayi Dantata tare da halartar jana’izarsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp