Wani mutum da har yanzu ba a tantance ko wanene ba ya mutu sakamakon wutar lantarki da ta rike shi a lokacin da yake kokarin sace wani abu a wata na’urar taransifoma a unguwar Ogbe, Ute-Okpu, ta Karamar Hukumar Ike Arewa-maso-gabas ta Jihar Delta.
Jaridar PUNCH Metro ta ruwaito cewa mazauna unguwar sun yi sanar da rasuwar tasa ne a lokacin da suka ga gawar mutumin a rataye a jikin sandar wutar lantarki da wayoyi da ke kusa da wata kasuwa a unguwar.
- Tsohon Wakilin LEADERSHIP Ya Zama Shugaban Gidan Rediyon Kano
- Kulla Dangantakar Diplomasiyya Tare Da Sin, Daya Ne Daga Cikin Kudurori Mafi Dacewa Da Kasar Tsibiran Solomon Ta Tsai Da A Tarihi
Wani mazaunin unguwar mai suna Mista John, ya shaida wa wakilinmu cewa, wani yaro da har yanzu ba a san ko wanene ba yana kan hanyarsa ta zuwa wata unguwa da ke kusa da wurin sai ya ga gawar a jikin sandar lantarki sai ya yi ihu.
John ya ce, “ Ya ce yaron yana kan hanyarasa ta ne ta zuwa kauye ya sanar da mu cewa ya ga gawa a rataye a kan sandar wutar lantarki. Domin mu tun safe muke cikin gida saboda ruwan sama da ake yi ba za a mu iya fita ba muna zaune a gadajenmu.
“ Ko da muka fito domin mu gane wa idanunmu abin da ya faru sai ba mu ga gawar matashin da ke rataye a wurin ba kamar yadda yaron nan ya bayyana masa domin gwar na rike da na’urar lantarki ta fado kasa.
“Mun dauki tsawon lokaci ba mu da wutar lantarki, sai wannan lokaci BEDC ta dawo da wutar da misalin karfe 3 na dare; Allah ne kadai ya san abin da ya faru. Mun sanar da ’yan banga a wannan yanki su kuma sun sanar da ’yansanda kafin daga nan aka zo a dauke gawar.”
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, DSP Bright Edafe, yaa tabbatar da faruwar lamarin.