Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Barcelona ta koma matsayi na biyu a kan teburin gasar La Liga ta Sifaniya bayan ta lallasa ƙungiyar Valencia a filin wasa na Johan Cruyff da ke birnin Barcelona.
Fermin Lopez, Raphinha da Lewandowski ne suka zura ƙwallaye shida a ragar Valencia a wasan da aka buga da misalin ƙarfe 8 na dare agogon Nijeriya. Da wannan nasara, Ƙungiyar da Hansi Flick ke jagoranta ta tara maki 10 a cikin wasanni huɗu da ta buga a gasar.
- Kano Pillars Ta Samu Nasarar Farko A Gasar Firimiyar Nijeriya Ta Bana
- Rashford Na Dab Da Komawa Barcelona A Matsayin Aro
An yi tsammanin Barcelona za ta fara buga wasan gidanta a sabon filin Spotify Camp Nou da aka gyara, amma sai mahukuntan Ƙungiyar suka yanke shawarar yin wasan a filin Johan Cruyff mai ƙarfin ɗaukar ‘yan kallo 6,000 kacal, wanda mafi yawan lokuta Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta mata Barcelona ke amfani da shi.
A gaba kuma, Barcelona za ta bakunci Newcastle United a filin wasa na St James’ Park a zagayen farko na gasar Zakarun Turai (UEFA Champions League) a ranar 18 ga Satumba. A gefe guda, Valencia za ta karɓi baƙuncin Atletico Bilbao a wasan mako na biyar na La Liga a ranar 20 ga Satumba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp