Kungiyar kwallon kafa ta FC Barcelona ta yanke shawarar korar kocinta, Xavi Hernandez daga aiki bayan wata tattaunawa da shugaban kungiyar, Joan Laporta ya yi da sauran mahukuntan kungiyar.
Xavi Hernandez ya lashe kofin Laliga,bCopa Del Rey da Spanish Super Cup a cikin shekaru biyu da rabi da ya shafe a tsohuwar kungiyar tasa, inda ya taka leda na tsawon shekaru fiye da 10.
- Kwastam Ta Cafke Kayan Fiye Da Naira Biliyan 3.1 A Shiyyar Kaduna
- ‘Yan Nijeriya Za Su Sha Wahala Matukar Ba A Biyan Alkalai Albashi – Babban Joji
Amma rashin nasarar da kungiyar ta Catalonia ta yi a hannun manyan abokan hamayyarta a bana da suka hada da Real Madrid da Paris Saint Germain a gasar zakarun Turai, ya matukar bata wa mahukuntan kungiyar rai,wanda hakan ya sa suke neman maye gurbin Xavi da wani wanda zai fishi kwazo a manyan gasannin kwallon kafa.
Ana hasashen tsohon kocin Bayern Munich dan asalin kasar Jamus, Hansi Flick ne zai maye gurbin Xavi a Barcelona.
Alaka ta fara tsami tun bayan wata magana da Xavi ya yi a kan matasan ‘yan kwallon Barcelona wadda ba ta yi wa Laporta dadi ba.
Yanzu Barcelona za ta mayar da hankalinta wajen neman wanda zai jagoranci kungiyar a kakar wasa mai zuwa don ganin ba ta maimaita abin da ta aikata a lokacin daukar Xavi Hernandez ba.