• English
  • Business News
Saturday, May 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Barkewar Cutar Lassa: Masana Sun Bayyana Hanyoyin Kare Kai

by Sani Anwar
2 months ago
in Labarai
0
Barkewar Cutar Lassa: Masana Sun Bayyana Hanyoyin Kare Kai
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A baya-bayan nan ne, cibiyar yaki da kula da cututtuka ta Nijeriya (NCDC), ta sake bayyana barkewar cutar zazzabin Lassa a jihohi 11 da kuma kananan hukumomi 63 da ke fadin wannan kasa.

An fara samun bullar wannan cuta ta zazzabin Lassa, tun a shekarar 1940 a Nijeriya, wanda da farko an yi kuskuren gano cutar a matsayin cutar cizon sauro. Kazalika, ana daukar wannan cuta ce, ta hanyar ci ko mu’amala da berayen da suka kamu da cutar ko fitsarinsu ko kuma wata najasa.

  • Wang Yi: Diflomasiyyar Kasar Sin Ta Samar Da Kwanciyar Hankalin Da Ake Bukata A Duniya Mai Cike Da Rikici
  • Matsalar Wuta Ta Jefa Wasu Sassan Nijeriya Cikin Duhu

Har ila yau, an fara killace wata ma’aikaciyar asibiti da ke dauke da wannan cuta ta Lassa a shekarar 1969, mai suna Laura Wine; wadda a karshe cutar ta yi ajalinta a Jihar Borno. An gano cutar a matsayin sabuwar kwayar cuta, wacce daga baya aka sanya mata suna cutar zazzabin Lassa. Cutar zazzabin Lassa, ta zama tamkar wata annoba a Nijeriya, inda take ci gaba da yaduwa lokaci bayan lokaci.

Cutar ta yadu a Kasashen Yammacin Afirka da dama da suka da Nijeriya, Laberiya, Sierra Leone, Guinea da kuma Ghana. Kazalika, an kuma bayar da rahoton bullar cutar a wasu sassan Afirka da Turai da kuma Arewacin Amurka, musamman ga matafiyan da ke dawowa daga wuraren da cutar ta bulla.

 

Labarai Masu Nasaba

Haraji: Amurka Ta Kama Hanyar Durkusar Da Kanta

Kotu Ta Ɗage Shari’ar Yahaya Bello Zuwa 26 Ga Yuni Don Yanke Hukunci

Manyan Wuraren Da Cutar Ta Bulla Da Kuma Kididdigar NCDC

Kamar yadda muka lakanto daga jaridar Blueprint, bincikensu ya nuna cewa, an samu bullar cutar zazzabin Lassan a shekarar 1970 a Nijeriya, inda sama da mutum 100 suka kamu da cutar.

A tsakanin 1989 zuwa 1990, bullar annobar cutar a Nijeriya, ta yi sanadiyyar kamuwar mutane akalla sama da 1,000. Haka nan kuma, a shekarar 2018 an sake samun bullar cutar a kasar, inda mutane sama da 1,500 suka kamu da cutar, sannan adadin wadanda suka kamun sun doshi kashi 20 cikin 100.

Kwana-kwanan ne, NCDC ta bayar da rahoton mutuwar mutum 80 daga cikin 413 da aka tabbatar sun kamu da cutar a cikin fadin jihohi 11 cikin mako shida daga 3 zuwa 9 ga watan Fabrairun 2025, bayan barkewar cutar a 2024, da sama da mutum 4,726 da suka kamu da cutar, inda dama daga cikinsu suka mutu.

Har wa yau, a rahotonta na baya-bayan nan, game da cutar zazzabin Lassa, NCDC ta bayar da rahoton mutuwar mutum 80 daga cikin 413 da aka tabbatar da sun kamu da cutar a jihohi 11 da suka hada da; Ondo, Taraba, Edo, Benuwe, Gombe, Kogi da kuma Ebonyi, inda ta ce; adadin wadanda suka kamu da cutar ya karu da kashi 19.4 cikin 100, daga kashi 17.5 cikin 100, duk dai a cikin shekarar 2024.

Hukumar ta kuma bayyana cewa, kashi 73 cikin 100 na wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar, sun fito ne daga Jihohin Ondo, Edo da Bauchi, in Ondo ke kan gaba da kashi 34 cikin 100, sai Edo da kashi 21 cikin 100, Bauchi kuma da kashi 18 cikin 100, inda ta bayyana cewa; adadin adadin kananan hukumomi 63 da ke cikin jihohi 11, sun tabbatar da kamuwa da cutar.

Har ila yau, NCDC ta kara da cewa, ba a samu rahoton ko mutum guda cikin ma’aikatan lafiya da ya kamu da cutar a cikin wannan makon ba. Kazalika, jinkirin gabatar da kararraki, ya taimaka wajen karuwar mace-macen da tsadar kudin magani da kuma karancin wayar da kan al’umma.

 

Matakan Da Aka Dauka

Domin magance barkewar cutar, NCDC ta ce; ta farfado da sakatariyar da ke kula da tsarurrukan da suka shafi wannan cuta ta zazzabin Lassa ta kasa (IMS), domin samun daidaito a ayyukan.

Ta kara da cewa, ta yi hadin gwiwa da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da Cibiyar Bincike ta Kasa da Kasa da wasu Cibiyoyin, don bunkasa hanyoyin gane cutar da kuma magance ta ba tare da wani bata lokaci ba.

Sannan, hukumar ta bukaci ‘yan Nijeriya da su dauki matakan kare kawunansu da suka hada da kula da tsafta, gujewa cudanya da berayen da ke dauke da cutar da kuma neman magani da wuri da zarar an ji alamu kamar na zazzabi, ciwon makogwaro da kuma zubar da jini babu gaira babu dalili.

Hukumar ta NCDC, ta kuma bukaci ‘yan Nijeriya da su yi taka-tsan-tsan wajen kamuwa da cutar, musamman ta hanyar adana abincin da aka rufe a cikin kwantena yadda ya kamata, don hana bera shiga. Kazalika, ta karfafi ‘yan Nijeriyan da su rika sanar da su tare kuma da daukar matakan kare kawunansu da sauran ‘yan’uwansu.

Hanyoyin Da Za A Bi Don Kare Kai

A wata hira ta musamman da aka yi da jaridar Blueprint, wani Farfesa a fannin cututtuka masu yaduwa da kwayoyin halitta a sashen nazarin halittu na Jami’ar Adeleke, Oladipo Kolawole ya bayyana cewa, akwai bukatar ‘yan Nijeriya su inganta tsarin sa ido, domin ganowa da kuma bayar da rahoton bullar wannan cuta ta zazzabin Lassa.

Ya ce, kamata ya yi a tabbatar an samu wadataccen sinadarin ‘ribabirin’, wanda shi ne maganin cutar zazzabin Lassan na farko, wanda hakan zai karfafa tare da taimakawa wajen warkar da masu dauke da cutar.

A cewar Farfesa Kolawole, gwamnatin tarayya karkashin Hukumar NCDC, na taka muhimmiyar rawa wajen daidaitawa tare da sa ido da ganowa da kuma mayar da martani a dukkanin fadin wannan kasa.

Ya kuma jaddada cewa, don gujewa barkewar zazzabin Lassa, ‘yan kasar za su iya daukar matakan kariya da dama, kamar gujewa cudanya da beraye, adana abinci da sarrafa shi yadda ya kamata, kasancewa cikin tsafta, gujewa cudanya da wadanda suka kamu da cutar da kuma wayar wa jama’a kai a koda-yaushe, domin kai kawunansu asibiti da wuri.

Kazalika, don rage barkewar cutar zazzabin Lassa a jihohi kamar su Edo, Ebonyi, Ondo da kuma Bauchi, Farfesan ya bayyana cewa, za a iya daukar matakai da dama da suka hada da karfafa tsarin sa ido da shigo da al’umma ciki, domin samun hadin kai da kuma kokarin daukar matakan kariya.

 

Wadane Matakai Ya Dace Gwamnati Ta Dauka

Wani likita mazaunin Birtaniya, a makarantar Chebening, wanda kuma ya kafa gidauniyar kiwon lafiya ta yara, Dakta Christian Inya Oko, ya shawarci gwamnatin tarayya ta kara zuba kudade tare da aiwatar da tsare-tsaren da za su taimaka wajen shawo kan wannan cuta ta zazzabin Lassa yadda ya kamata. Ya ce, ya rasa abokansa likitoci da dama sanadiyyar wannan cuta, baya ga sauran ‘yan Nijeriya da ba su ji ba, ba su gani ba.

Ya ce, “Bayan mutuwar abokaina likitoci uku tare da wasu ‘yan Nijeriya sama da 800 da suka kamu da cutar zazzabin Lassa, na kadu matuka da jin rahoton NCDC na baya-bayan nan. A rahoton shekara ta 2024, Cibiyar Kula da Cututtuka ta Kasa (NCDC), ta bayar da rahoton kusan mutum 1300 da aka tabbatar da sun kamu da cutar, kashi 16.3 cikin 100 na mace-mace, wato mutum 214 da suka mutu a jihohi 28.

Jihohin Edo, Ondo da Bauchi ne ke kan gaba a jerin sunayen, yayin da Taraba, Ebonyi, Enugu da Filato, su ma suka bayar da rahotanni marasa dadi. A cikin mako na shida na 2025, an samu mutuwar mutum 80 cikin mutum 413 da suka kamu da cutar a jihohi 28 tare da karin mutuwar mutum 10 a cikin wannan makon.

“Idan aka yi la’akari da wannan kididdigar, akwai bukatar kara ingancin matakan da ake amfani da su wajen kokarin dakile wannan cuta ta zazzabin Lassa. Zazzabin Lassa, wani muhimmin al’amari ne da ya shafi lafiyar al’umma a Nijeriya da ake fama da shi”, in ji shi.

Dakta Oko ya yi nuni da cewa, ya kamata a samar da hanyoyin horar da ma’aikatan kiwon lafiya a cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko da na sauran manyan makarantu, don ganowa da magancewa da kuma kaucewa ire-iren wadannan kwayoyin cututtuka. Marasa lafiyan da aka gano suna dauke da cutar, ya kamata a ba su kulawa ta musamman, ta hanyar ba su magunguna da sauran abubuwan da suka dace, har sai sun warke.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: CutaLassaZazzabi
ShareTweetSendShare
Previous Post

Hajjin 2025: Ba Zan Taba Bai Wa Tinubu Da ‘Yan Nijeriya Kunya Ba – Shugaban NAHCON

Next Post

Kwararru Sun Nuna Fargaba Kan Yadda Wasu Makiyaya Ke Bai Wa Dabbobinsu Magunguna Barkatai

Related

Haraji: Amurka Ta Kama Hanyar Durkusar Da Kanta
Ra'ayi Riga

Haraji: Amurka Ta Kama Hanyar Durkusar Da Kanta

11 hours ago
Kotu Ta Ɗage Shari’ar Yahaya Bello Zuwa 26 Ga Yuni Don Yanke Hukunci
Labarai

Kotu Ta Ɗage Shari’ar Yahaya Bello Zuwa 26 Ga Yuni Don Yanke Hukunci

13 hours ago
Masana Sun Bayyana Ingancin TELA Maize Ga Rayuwar Al’umma
Noma Da Kiwo

Masana Sun Bayyana Ingancin TELA Maize Ga Rayuwar Al’umma

14 hours ago
Hukumar Raya Arewa Maso Yamma Ta Soke Shirin Tallafin Karatun Ƙasashen Waje
Labarai

Hukumar Raya Arewa Maso Yamma Ta Soke Shirin Tallafin Karatun Ƙasashen Waje

15 hours ago
GORON JUMA’A 09/05/2025
Labarai

GORON JUMA’A 09/05/2025

16 hours ago
AIRLIN Ta Buƙaci Ƴan Arewa Su Ƙara Ƙaimi Wajen Rijistar Katin Zaɓe Da Na Shaidar Ɗan Ƙasa 
Labarai

AIRLIN Ta Buƙaci Ƴan Arewa Su Ƙara Ƙaimi Wajen Rijistar Katin Zaɓe Da Na Shaidar Ɗan Ƙasa 

17 hours ago
Next Post
Kwararru Sun Nuna Fargaba Kan Yadda Wasu Makiyaya Ke Bai Wa Dabbobinsu Magunguna Barkatai

Kwararru Sun Nuna Fargaba Kan Yadda Wasu Makiyaya Ke Bai Wa Dabbobinsu Magunguna Barkatai

LABARAI MASU NASABA

Likitocin Sin Sun Ba Da Jinya Kyauta A Yankunan Karkara Na Saliyo

Likitocin Sin Sun Ba Da Jinya Kyauta A Yankunan Karkara Na Saliyo

May 9, 2025
Babban Bankin Sin Zai Inganta Hidimomin Kudi Don Habaka Amfani Da Shi

Babban Bankin Sin Zai Inganta Hidimomin Kudi Don Habaka Amfani Da Shi

May 9, 2025
Sin Da Rasha Sun Fitar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Game Da Zurfafa Dangantakar Abokantaka Ta Hadin Gwiwa Bisa Manyan Tsare-tsare A Sabon Zamani

Sin Da Rasha Sun Fitar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Game Da Zurfafa Dangantakar Abokantaka Ta Hadin Gwiwa Bisa Manyan Tsare-tsare A Sabon Zamani

May 9, 2025
Hukumar Fina-Finai Ta Kasar Sin Ta Kulla Takardar Hada Hannu Da Hukumar Al’adu Ta Kasar Rasha

Hukumar Fina-Finai Ta Kasar Sin Ta Kulla Takardar Hada Hannu Da Hukumar Al’adu Ta Kasar Rasha

May 9, 2025
Haraji: Amurka Ta Kama Hanyar Durkusar Da Kanta

Haraji: Amurka Ta Kama Hanyar Durkusar Da Kanta

May 9, 2025
Kotu Ta Ɗage Shari’ar Yahaya Bello Zuwa 26 Ga Yuni Don Yanke Hukunci

Kotu Ta Ɗage Shari’ar Yahaya Bello Zuwa 26 Ga Yuni Don Yanke Hukunci

May 9, 2025
Masana Sun Bayyana Ingancin TELA Maize Ga Rayuwar Al’umma

Masana Sun Bayyana Ingancin TELA Maize Ga Rayuwar Al’umma

May 9, 2025
Hada-hadar Cinikayyar Waje Ta Kasar Sin Ta Karu Da Kaso 5.6 Bisa Dari A Watan Afirilu

Hada-hadar Cinikayyar Waje Ta Kasar Sin Ta Karu Da Kaso 5.6 Bisa Dari A Watan Afirilu

May 9, 2025
Hukumar Raya Arewa Maso Yamma Ta Soke Shirin Tallafin Karatun Ƙasashen Waje

Hukumar Raya Arewa Maso Yamma Ta Soke Shirin Tallafin Karatun Ƙasashen Waje

May 9, 2025
GORON JUMA’A 09/05/2025

GORON JUMA’A 09/05/2025

May 9, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.