Gwamnatin jihar Kano ta ce gwamnatin da ta shude karkashin jam’iyyar APC ta Abdullahi Umar Ganduje ta bar bashin sama da Naira biliyan 500, lamarin da ya kawo cikas wajen fara ayyuka ga gwamnatin NNPP.
Mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ne, ya bayyana hakan a Kaduna ranar Juma’a yayin da yake jagorantar taron shiyyar Arewa maso Yamma na NNPP.
- Ministan Wajen Sin Ya Yi Kira Da A Tsagaita Wuta A Gaza
- NLC Za Ta Shiga Yajin Aiki Kan Cin Zarafin Shugabanta, Ajaero
A cewarsa, dimbin basussukan da gwamnatin da ta shude ta bari, ya haura naira biliyan 500.
Ya bayyana irin nasarorin da sabuwar gwamnatin NNPP karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta cimma cikin kankanin lokaci a karagar mulki.
Abdussalam ya kuma tabbatarwa da mambobin jam’iyyar a wurin taron cewa gwamnatin da NNPP ke jagoranta ba za ta yi kasa a guiwa wajen biya musu bukatunsa ba.
“Mun gaji bashi da yawa,” in ji shi.
Ya kuma bayyana irin kokarin da gwamnatin jihar Kano mai ci ke yi wajen tafiyar da albarkatun da ake da su cikin adalci, inda ya ce.
“Bugu da kari kuma, saboda tausayin Gwamna Abba Kabir Yusuf, daga wannan watan, za a fara bada kudin fansho, musamman ga iyalan wadanda suka rasu.
“Wadanda za su fara cin gajiyar shirin za su kasance daga mataki na daya zuwa na shida, saboda kananan ma’aikata ne da suka fi shan wahala. Mun ware Naira biliyan shida don biyan su.
“Ana ci gaba da aikin tantance su, kuma daga karshen wannan wata, mutane da yawa za su samu kudinsu.”