ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hanyoyin Kare Lafiya Lokacin Hunturu – Dakta Sufyan 

by Shehu Yahaya
3 years ago
Hunturu

LABARAI MASU NASABA

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

Kotu Ta Tsare Shugaban Makaranta Da Malami Kan Zargin Lalata Da Ɗaliba Mai Shekara 6 A Gombe

Lokacin huturu, lokacin ne da jiki da fatar mutane ke wahala matuka saboda kura da iskar da ake yawan fama da ita.

Kamar yadda aka sani hunturu kan fara ne a tsakanin watan Nuwamba zuwa Maris. A irin wannan lokaci fatar mutane kan rika yakunewa yana karkarcewa wasu ma har yankewa yake wato abin da ake kira da fasau a kafar mutane.

  • Yadda Rakiyar Gwamnan Kano Ga Tagwayen da ke Manne Da Juna Ta Dauki Hankalin Al’umma
  • Hukumar Alhazai Ta Jihar Kebbi Ta Samu Sabon Shugaba

Matsalolin da irin wannan canjin yanayin ke kawowa sun hada da bashewar leben baki, tsagewar kafafen hanci, mura da dai sauran su matsaloli da ke yi wa lafiyar jiki illa.

Masana harkar lafiya sun bayyana irin matakan da ya kamata mutane su bi domin rigakafi yayin shigowar hunturu, inda suka ba da shawarar a rika saka kaya masu nauyi kuma wadanda ke rufe jiki kaf da takalma da za su rufe kafafuwa domin kare mutum daga iska.

Sun ci gaba da cewa akwai bukatar mutane su rinka shafa man kade, domin shi man kade na da ingancin hana bushewar jiki.

Wakilinmu ya zanta da babban likitan asibitin Na Kowa da ke Marabar Jos a cikin karamar hukumar Igabi ta Jihar Kaduna, Dakta Sufyan Umar Yari ya bayyana cewa, “Abin da ya kamata a duba shi ne, wadanne irin cututtuka ne aka fi samu lokaci sanyi kan manyan mutane da kuma kananan yara. Idan muka lura yanayin yana canzawa, ya kan zo da kura da iska kuma yana iya zuwa da tsananin sanyi.

“Mafi akasari dai an fi samun cututtuka da suka fi alaka da huhu irin su cutar nimoniya da asma wacce ba cuta ba ce da ake dauka a tsakanin mutane, amma dai ta fi ta shi a lokacin sanyi, saboda abin da ke ta da ta shi ne iska ko kura ko kuma shan wani abu mai sanyi,” in ji shi.

Dakta Sufyan ya ci gaba da cewa cutar nimoniya ga kananan yara ta fi tashi lokacin hunturu. Likitan ya bukaci iyaye da su takaita zirga-zirgan ‘ya’yansu da safe da kuma kula da irin kayan da ake saka musu, idan ya zama dole su fita, sai a rika saka musu kayan sanyi.

Haka zalika, ya ce, “Akwai babban kuskure da mutane suke yi lokacin hunturu na kai wuta daki ko kuma rufe daki a hana iska shigawa. Irin wannan yana haifar da matsala, saboda maimakon a kare jiki da sanyi sai kuma wata cuta da shiga. Babu wata ka’ida da ta nuna cewa dole sai mutum ya rufe ko ina kafin ya kwanta barci.  Yana iya haifar da matsala musamma idan aka rufe ko ina kuma an kai wuta dakin domin shan dumin daki, to wannan abu yana haifar da matsaloli sosai.”

“Akwai magana ta wanka da ake yi wa yara a wannan lokacin hunturu, ya zama dole a rika neman dumaman ruwa ba ruwa tafasashshe ba, maimakon a yi wa yaro wanka sai a kona shi, wanda muna cin karo da irin wadannan matsaloli. Sai ka ga an kawo musu asibiti a galabaice wanda sai da kyara ake ceto rayuwarsu. An fi samun cututtuka irinsu nimoniya da bushewar makoshi da asma a lokacin hunturu, ” in ji shi.

Ya ce idan lokacin hunturu ya zo, suna bai wa mutane shawarar da rinka yawaita shan ruwa. A cewarsa, fatar Dan’adam tana aiki da ruwa, rashin yawaita shan ruwa yana haifar da tamukewar fata da bushewar makoshi.

Wasu magidanta a Jihar Kaduna sun bayyana irin hanyoyin da ya kamata a bi domin kare jiki da kamuwa daga wasu cututtukan lokacin hunturu.

 Muhammadu Abdullahi magidanci ne da ke zaune a unguwar Dosa a Kaduna, ya ce lokacin hunturu akwai bukatar mutane su rika yin wanka da ruwan dumi musamman da safe ko kuma da yamma.

Ya ce za a iya cin abincin da ke dauke da kitse, fiya, kifi domin suna dauke da sinadarin da ke gyara fatar mutum.

“Kamar ni ina tabbatar da cewa kamin yarana su tafi makaranta, sai an saka musu kayan sanyi da kuma ba su abinci mai dumi. Haka ni kaina da matata duk irin matakan da muke dauka kenan lokacin hunturu. Ka ga dai yau mun tashi babu rana sai iska da hazo, wanda ya zama dole a gare ni na samar wa kaina mafita wato zan sa yi gilashi na ido da talakli mai rufi da dai sauran,” in ji shi.

Wata matar aure, Fatima Ibrahim ta ce rashin ko-in-kula da wasu iyaye mata suke yi a kan yaransu yana haifar da lalurori da yawa kama daga kamuwa da mura da masassara wadanda cututtuka ne da suke hana yara sukuni.

Ta ce a matsayinta ta uwa tana daukar matakan sanya kayan sanyi ga yaranta yayin zuwa makaranta da kuma kiyaye irin abincin da suke ci.

Fatima ta shawarci gwamnatoci da su samar da magunguna, musamma ga yara a asibitoti wanda a lokaci hunturu yara kan iya shiga halin kunci fiye da manya.

Sai dai a wani bincike da wakilinmu ya gudanar a ma’aikatar kiwon lafiya ta Jihar Kaduna, ya gano cewa lokacin hunturu ko sanyi kwakwalwar Dan’adam za ta dunga sa tsokar jiki ta rinka motsawa da sauri-sauri, wanda ake kira rawar sanyi. Amfanin hakan shi ne, samar da zafi wanda zai dumama jiki saboda haka a duk sanda wata gaba ke aiki a jikin mutum, to zafi na samuwa ta ciki kamar yadda idan ka kunna na’urar za a samu zafi.

Binciken ya nuna cewa, wannan yawan motsawar tsoka a cikin sauri lokacin da mutum ke rawar sanyi ita ce hanyar da jiki ke samar wa kansa dumi, sannan kuma a kokarin jiki na kare shigar cututtuka ta hanyar iskar da muke shaka, ya sa majina ke fita daga hancinmu.

An gano cewa a cikin iska akwai datti da kura da cututtuka iri-iri, zarar mun shaki irin wannan iskar, kwayoyin halitta da ke bututun iska da makogwaro za su gane cewa ka shaki gurbatacciyar iska, nan da nan bututun iska wanda ya fara daga kofofin hanci zuwa cikin huhu, sai ya fara samar da majina.

Hunturu
Shehu Yahaya
+ postsBio
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Majalisar Zartarwa Ta Jihar Kaduna Ta Amince Da Manufofin Haɓaka Walwalar Al’ummar Jihar
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Rashin Tarbiyya Da Ilimin Addini Ne Ke Sa Matasa Ɗaukar Doka a Hannu – Hon. Aminu Adam
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Yadda Ayyukan Titunan Gwamnan Kaduna Suka Farfaɗo Da Ilimi Da Kiwon Lafiya Da Noma A Sabon Gari
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Abubuwan Da Ba A Faɗa Ba Game Da Yadda Aka Hallaka Malamar Islamiyya A Kaduna
ADVERTISEMENT

MASU ALAKA

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu
Labarai

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

July 14, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga
Manyan Labarai

Kotu Ta Tsare Shugaban Makaranta Da Malami Kan Zargin Lalata Da Ɗaliba Mai Shekara 6 A Gombe

July 14, 2026
Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi
Labarai

Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

July 14, 2026
Next Post
CIIE: ‘Yan Kasuwan Kasa Da Kasa Na Alla-alla Wajen Yin Amfani Da Damar Ci Gaban Kasar Sin

CIIE: ‘Yan Kasuwan Kasa Da Kasa Na Alla-alla Wajen Yin Amfani Da Damar Ci Gaban Kasar Sin

LABARAI MASU NASABA

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

July 14, 2026
Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

July 14, 2026
An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

July 14, 2026
Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

July 14, 2026
Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

July 14, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Kotu Ta Tsare Shugaban Makaranta Da Malami Kan Zargin Lalata Da Ɗaliba Mai Shekara 6 A Gombe

July 14, 2026
An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

July 14, 2026
Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

July 14, 2026
Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

July 14, 2026
CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

July 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.