A kwanakin baya ne aka sanya hannu kan dokar bayar da bashin dalibai da kuma yadda aka ware kudi kimanin naira biliyan hamsin, a cikin kasafin kudin shekarar 2024, domin bayar da rancen dalibai. Duk da dai, manufofin da ke bayan kudirin na da kyau.
Kazalika, nazari ya tabbatar da cewa, manufar ba za ta haifar da da mai ido ba, yayin da kuma tunani da hasashe ya nuna rashin adalci da inganci da kuma mummunar manufa ga jin dadin daliban Nijeriya da sauran ‘dan kasa.
- Sin Za Ta Dauki Matakan Da Suka Dace Kan Kamfani Da Wasu Mutanen Amurka Da Suka Shafi Batun Xinjiang
- Kasar Sin Ta Ware Yuan Miliyan 400 Don Taimakawa Wadanda Bala’in Girgizar Kasa Ta Shafa A Gansu Da Qinghai
Sharuddan Bayar Da Bashin
Uku daga cikin sharuddan samun wannan rance na da matukar tsauri, wanda zai iya iyakancewa maimakon karfafa masu neman izini. Wadannan su ne na daya, mai garantin ma’aikacin gwamnati mai mataki na 12 ko kuma mutum mai daraja, yanzu mutum nawa ne ke da ma’aikaci mai daraja 12 a cikin danginsu ko kuma wani mutum mai daraja wanda kuma yake son daukar irin wannan nauyi?
Na biyu, dalibin da zai rattaba hannu a kan alkawarin biyan bashin a cikin wani kayyadadden lokaci, wa ke da tabbacin gobe idan aka yi la’akari da manufofin da gwamnati ke furtawa babu zato babu tsammani?
Na uku, dole ne dalibai su bi dukkanin wasu sharudan da hukumar lamuni ta dalibai za ta gindaya musu, wannan yana nuni ne da canza “dokokin bayar da bashin rana tsaka”. Kar a yi maganar cikas na ofisoshi da ke da alaka da kowane talafi na gwamnati da yanayin siyasar Nijeriya.
Kalubalen Da Dalibai Da Iyaye Za Su Fuskanta
Duk da makudan kudaden da aka ware, matsalolin da za a fuskanta wajen samun wannan lamuni na da matukar yawa. Bugu da kari, ka’idojin da aka gindaya na nuna cewa, bashin na da riba a cikinsa.
Damar Da Aka Rasa Da Manyan Tambayoyi
Biliyan hamsin(50) na da yawa, amma duk na rance ne ko kuma babban kaso ya shafi kayayyakin more rayuwa da suka shafi hukumar bayar da bashin ne? Hakan ya sa ayar tambaya a kan abubuwan da gwamnati ta sa a gaba. Idan manufar ita ce a taimaka wa dalibai don neman ilimi mai zurfi, me zai hana a ware wadannan kudade a matsayin tallafi maimakon bashi?
Sakamakon Rashin Kishin Kasa
- Kamar yadda aka tsara a halin yanzu, rancen yana iya haifar da damuwa game da yiwuwarsa na habaka halin rashin kishin kasa a tsakanin matasa. Don haka, ya kamata gwamnati ta sanya hannun jari a harkar iliminsu a matsayin fifikon kasa, abin bakin ciki shi ne; gwamnati na fuskantar kasadar samar da tsarurraka masu daukar ilimi a matsayin mu’amala, maimakon hada hannun jari a makomar kasa.
- Aiwatar da kudirin rancen dalibai, wani lamari ne wanda ke nuni da rashin tausayawa daga bangaren jami’an gwamnati. Wadannan jami’ai, a lokacin karatunsu; sun ci gajiyar tallafin karatu kyauta tare da bayar da tallafin karatu da walwala iri daban-daban. Bambance-bambancen da ke tsakanin abubuwan da suka samu da kuma kalubalen da ke tattare da kudirin rancen daliban; ya sanya ayar tambaya a kan yadda gwamnati ke kokarin kyautata rayuwar al’ummarta.
III. Raba kudade a matsayin rancen dalibai ya bambanta sosai da abubuwan da aka ware a wasu wurare cikin kasafin kudi. Makudan kudaden da aka ware domin sayen Jif-jif, gina wa mataimakin shugaban kasa gida na nuna rashin fifiko da bai dace da ka’idojin mulki ba.
Mu Kwatanta Alfanun Bashi Da Sikolashif Mu Gani:
- Rashin Daidaito:
- Lamunin dalibai zai haifar da cikas ga dalibai masu fama da matsalar tattalin arziki.
- Sikolashif/tallafin dalibai na makaranta na magance rarrabuwar kawuna ta hanyar bayar da taimakon kudi ba tare da nauyin biyan bashi ba. Wannan yana tabbatar da cewa duk dalibi, ba tare da la’akari da yanayin tattalin arzikinsa ba, na da damar samun ingantaccen ilimi. (Shin wannan bai kamata ya zama ma’auni mafi dacewa ba?)
- Ingantaccen Amfani Da Albarkatu:
- Tsarin lamuni na dalibi, na bukatar ingantaccen kayan aikin gudanarwa, gami da kirkirar hanyoyin bayar da lamuni, bin diddigi da tarawa. Wannan aikin gudanarwa; tabbas zai karkatar da albarkatu daga burin farko na tallafa wa ilimi.
- Sikolashif ya fi daidaitawa ta fuskar gudanarwa. Kudaden na tafiya ne kai tsaye ga dalibai tare da rage sarkakkiya a tsarin mulki da tabbatar da ingantaccen rabon albarkatu, don neman ilimi.
- Karfafa Tattalin Arziki Da Ci Gaban Kasa:
- Lamunin dalibai zai kawo tsaiko wajen bayar da gudunmawar tattalin arzikin da ‘ƴan kasa masu ilimi za su bayar, don ci gaban kasa domin abin damuwa zai fi yadda za a biya ko kuma kaucewa biyan kudin.
- Sikolashif/tallafi, wadanda suka kammala karatunsu ba tare da bashi ba sun fi bayar da gudummawa ga ci gaban tattalin arziki ta hanyar kasuwanci, kirkire-kirkire tare da sanya hannun jari a kan lokaci cikin al’ummominsu.
Ina Mafita?
- Gabatar da guraben karo karatu mai inganci, domin kwadaitar da nagartar ilimi, domin zaburar da dalibai su himmatu wajen kara kwazo tare da bayar da gudumawa ga al’umma.
- Kara yawan kasafin kudi ga Ilimi tare da karkatar da wani bangare nasa zuwa guraben karo karatu, tallafi da kuma inganta ayyukan ilimi baki-daya.
III. Hadin gwiwar gwamnati da kanfanoni masu zaman kansu, domin habaka kokarin gwamnatin ta hanyar gabatar da sabbin nau’ikan tallafin kudi.
A karshe:
A cewar Nelson Mandela, “Ilimi shi ne makami mafi karfi, wanda zaka iya amfani da shi don canza duniya baki-daya.”Mu yi amfani da wannan makami cikin hikima da adalci, domin ci gaban al’ummar Nijeriya.
Alhaji Adamu Rabiu ya rubuto daga Kaduna.