Mutane kalilan ne suka san shi a shekarar da ta wuce, amma yanzu ya shirya zama shugaban kasa.
Tashen ban al’ajabi na Bassirou Diomaye Faye, wani lokaci ne mai cike da hawa da gangara a tarihin siyasar Senegal, da kuma ya zo da mamaki ga mutane da dama.
- Idan Aka Fatattaki ‘Yan Ta’adda Daga Zamfara Duk Arewa Za Mu Samu Sauki – Gwamna Dauda
- Xi Jinping Ya Taya Bassirou Diomaye Faye Murnar Zama Shugaban Senegal
Watannin da ya shafe tsare a gidan yari tare da babban abokin siyasarsa kuma uban-gidansa Ousmane Sonko sun zo karshe a yayin da ya rage mako daya a yi zaben shugaban kasar.
A yanzu Mai gaskiya, kamar yadda ake yi masa lakabi, zai iya fara aiki kan manyan sauye-sauyen da ya yi alkawarin kawowa a lokacin yakin neman zabe.
“Mai tabbatar da bin tsari” da “kas-kas da kai” su ne kalmomin da aka fi amfani da su wajen bayyana jami’in karbar harajin, wanda ke bikin cikarsa shekara 44 da haihuwa.
Mallam Faye cikin murna ya kan tuna rayuwar kuruciyarsa ta kauye a Ndiaganiao, inda ya ce ya kan kai ziyara a duk ranar Lahadi don yin aiki a gona.
Kaunarsa da darajar da yake bai wa rayuwar mutanen karkara sun dace da zuzzurfan rashin amincewarsa da manyan kasa a Senegal da kuma tsarin siyasar da aka saba da ita.
“Bai taba rike mukamin minista ba, kuma shi ba gogaggen jami’in gwamnati ba ne don haka masu suka suke tuhumar rashin gogewarsa,” kamar yadda mai sharhi Alioune Tine ya faka wa BBC.
“Sai dai, fahimtar Faye, jami’an da suka tafiyar da harkokin mulkin kasar tun daga 1960 sun tafka manya-manyan kura-kurai.”
Yaki da fatara da rashin adalci da kuma cin hanci na cikin manyan manufofin Mallam Faye. Da yake aiki a Baitulmali, shi da Ousmane Sonko sun kafa wata kungiyar ko-ta-kwana don tunkarar masu cin hanci da rashawa.
Yarjeniyoyin hakar iskar gas da man fetur da kuma na tsaro jazaman ne sai an sake cimma matsaya a kan su don su biya muradan al’ummar Senegal, in ji Mallam Faye.
Yana kokarin kawo wani zamani na “gwamnati mai cikakken iko da “birkita al’amura” sabanin yadda aka saba yi a baya, kamar yadda ya faka wa masu zabe, da kuma mu-samman hakikanin alakarsu da Faransa.
Zababben shugaban kasar na Senegal ya ce zai yi watsi da kudin saifa na Faransa da ake yawan sukar lamiri, wadda ake kwatanta darajarta da yuro sannan take samun goyon bayan Faransa, tsohuwar uwargijiyar mulkin mallakar Senegal.
Mallam Faye dai yana son maye gurbin saifa da wani sabon kudin Senegal ko na yankin Afirka ta Yamma, ko da yake hakan ba abu ne mai sauki ba.
“Zai ci karo da kalubalen hakikanin al’amura kamar na kasafin kudin a farkon farawa… Sai dai na lura shi mutum ne mai kumbin buri,” tsohuwar Firaminista Aminata Toure wadda ta yi aiki a karkashin shugaba mai barin gado Macky Sall ta bayyana wa BBC.
Karfafa ‘yancin cin gashin kai ga bangaren shari’a da samar da ayyuka ga dumbin mata-san Senegal su ma suna cikin manyan manufofin Mallam Faye – dukkansu biyun dai “ba su samu wata kyakkyawar kulawa ba daga Shugaba Sall, alhakin hakan kuma sai da ya kama shi”, Aminata Toure ta kara da cewa.
Ba ita ce kadai babbar ‘yar siyasa da ta mara baya ga matashin kan shekara 44 ba – tsohon shugaban kasar Abdoulaye Wade shi ma ya yi hakan kwana biyu kacal kafin zaben ranar Lahadi.
Wani gagarumin sauyin rayuwa ne ga Mallam Faye bayan ya shafe wata 11 da ya wuce tsare a gidan yari bisa tuhume-tuhumen bore da kuma shekaru da dama kafin nan a karkashin siyasar abokiyar tafiyarsa.
‘Bassirou da ni abu daya ne’.
A cikin watan Fabrairu ne aka sanar da Bassirou Diomaye Faye a matsayin abin da aka kira kan takarar “idan hagu ta kiya, a koma dama”, don maye gurbin jagoran ‘yan adawa mai kwarjini da kwakwazo, Osumane Sonko. “Zan iya cewa ya fi ni kokarin kamanta gaskiya,” Sonko ya ce cikin alfahari.
Su biyun ne suka kafa rusasshiyar jam’iyyar Pastef, su biyun kuma sun kasance jami’an karbar haraji, kuma dukkansu sun samu kansu a gidan kurkuku bara a kan tuhume-tuhumen da suka ce suna da alaka da siyasa.
A karshe dai an samu Ousmane Sonko da aikata laifuka guda biyu, abin da ke nufin hana masa damar tsayawa takara a zabe, don haka sai Mallam Faye ya shige gaba.
“Ni da Bassirou duk daya ne,” Mallam Sonko ya fada wa taron magoya baya cikin ‘yan kwanakin nan. “Manyan aminan juna ne,” in ji Moustapha Sarre wani takwaransu a jam’iyyar Pastef ya bayyana.
Hakan ta sanya ana sukar lamirin cewa Mallam Faye kawai zai kasance ne “shugaban kasa ne na je-ka-na-yi-ka”.
Ba lallai hakan ta kasance ba, a cewar mai sharhi Mista Tine. Sai dai dangantakar mu-tanen biyu za ta iya kawo wani sabon salon shugabanci a Senegal.