Batun cunkoson Gidajen Gyara Hali a fadin Nijeriya na ci gaba da zama cikin abubuwan tattaunawa a wurare da dama na harkokin al’umma a fadin kasar nan. Ga wadanda basu san cikakken halin da gidajen yarin suke ciki ba, har yanzu su na nan a halin da turawan mulkin mallaka suka samar da su a shekarun baya kafin su koma kasashen su da sunan bamu ‘yancin kai. Chanza sunan su daga yadda aka san su a da tunda farko na ‘Nigerian Prison Serbice (NPS)’ zuwa ‘Nigerian Correctional Serbice’ bai nuna wani canji daga yadda aka san su a daba a cikin tsarin hukunce-hukuncen shari’a na Nijeriya.
A farko an tsara zaunar da daurarru masu laifi 50,000 ne a gidajen gyaran halin amma a halin yanzu gidajen yarin kasar nan na dauke ne da masu laifi fiye da mutum 73,000.
Tabbas wannan cunkoson ya haifar da matsaloli da daman gaske wadanda suka hada da rashin tsafta, rashin samun kulawa ta magunguna ga marasa lafiya da kuma yadda ake samun karuwa cututtuka da kuma yadda daurarrau ke kara kangarewa bayan sun fito daga wadannan gidajen gyaran halin fiye da yadda suka shiga tunda farko.
Amma kuma cikin manya-manyan matsalolin da ake fuskanta su ta na yadda ake samun karuwar daurarun da ke jiran hukuncin kisa. Kwanaki Hukumar Kula da Gidajen Gyaran halin ta fitar da bayanin cewa a halin yanzu akwai fiye da mutum 3,298 da ke jiran a yanke musu hukuncin kisa a gidajen yari daban-daban a fadin kasar nan. Jami’in Watsa Labaran Hukumar, Abubakar Umar, ya bayyana cewa, ba a cika gaggauta zartar da hukuncin kisa ba da zaran an yanke ba.
Ya kara da cewa, ana daukar dogon lokaci a saboda yadda ake samun daukaka karar hukuncin da aka yanke a manyan kotuna.
“Wasu masu laifin kan yi jiran fiye da shrekara 15 kafin a yanke musu hukuncin. Suna nan suna jiran a zo a yanke musu hukuncin kisan kamar yadda kotu ta yanke. Muna na da su da dama, a yanzu a kwai mutum 3,298 da ke jiran hukuncin kisa. Su ne kusan kashi 4.5 na yawan daurarrun da muke da su a gidajen gyaran hali a fadin kasar nan,” in ji shi.
Tabbas hukuncin kisa wani abu ne da aka ci gaba da takaddama a kai, wasu na ganin alfanunsa wasu kuma na ganin bashi da wani amfani a tsarin ladaftar da rayuwar al’umma suna kuma kira da a gaggauta soke shi gaba daya.
Ra’ayin wannan jaridar a nan shi ne, duk kuwa da ra’ayin da wani yake da shi a kan hukuncin kisan, a bayyana yake cewa, bai kamata a bar daurarrau masu jiran hukuncin kisa su dauki dogon lokaci suna jiran a yanke musu hukucin ba, wannan ba a bin da za a amince da shi ba ne.
A lokutta da dama a barin dauraru masu jiran hukuncin kisa su dade na tsawon sherkaru ba tare da da sanin halin da suke ciki ba, wannan rashin adalci ne garesu da iyalansu da kuma al’umma gaba daya.
Daya daga cikin abin da ke haifar da wadannan matsalolin shi ne kin gwamnoni na sanya hannu a takardar hukuncin zartar da hukuncin kisan. Amma a yanzu wasu gwamnoni da dama suna jinkirin sanya hannu a kan takardar hukuncin kisan saboda abubuwan da suka shafi siyasa da sauransu. Wannan ya sanya dauraru da ke jiran hukuncin kisa suke ci gaba da zaman jiran dirshan ba tare da sanin yaushe za a yanke musu hukuncin ba.
Ida za a iya tunawan tun da aka dawo mulkin farar hula a shekara 1999, gwamnoni 2 ne kawai suka sanya hannu a kan zartar da hukuncin kisa ga daurarru na fadin kasar nan.
Za kuma a iya tunawa da cewa, tsohon gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau ne na farko da ya sanya hannu a zartar da hukuncin kisa a shekarar 2006, yayin da Gwamna Adams Oshiomhole ya zama na biyu a shekarar 2012.
Tsohon gwamnan Kano ya zartar da hukuncin kisan wasu dauraru ne da ake jiran hukuncin kisa a inda aka zartar musu da hukuncin ba tare da bata lokaci ba, yayin Oshiomhole ya sa hannu a kisan mutum biyu a jiharsa ta Edo.
Yayin da za a iya amincewa da ana iya samun gwamnonin da suke adawa da hukuncin kisa amma ya kuma kamata a fahimci cewa, tuni kotu ta samu wadannna mutanen da laifukkan da ake zargin da su kuma ta yanke musu hukuncin na kisa.
A ra’ayinmu, kin sanya hannu a hukuncin kisan da gwamnoni suke kin yi kamar suna danne hukucin kotuna ke nan wanda hakan kuma yana nuna suka katsalandan ga hurumin kotunan ke nan. Wannan kuma ba adalci ne ba ga daurarun kuma yana nuna cewa, za a iya amfani da karefin siyasa wajen canza hukunce-hukuncen da kotuna suke yankewa a kasar nan.