Cibiyar daidaita mummunar manhajar dake bata kamfuta ta kasar Sin da kamfanin 360 na kasar Sin, sun gabatar da wani rahoton bincike a yau Alhamis, wanda ya yi bayani game da batun kai hari kan sauran kasashe da hukumar leken asiri ta kasar Amurka wato CIA ta yi ta yanar gizo.
Rahoton ya kuma yi bayani kan batutuwan kiyaye tsaron yanar gizo dake faruwa a kasar Sin da wasu kasashen duniya, tare da nazari kan ayyukan leken asiri na hukumar CIA, da gudummawar da ta bayar ga kasar Amurka na kasancewa kasa mai leken asiri ta yanar gizo. Rahoton zai zama abin misali da shawara ga masu gamuwa da harin yanar gizo daga sassan duniya. (Zainab)
Talla