Kamar yadda aka fadi a baya cewa, mai magana da yawun hukumar, Olumuyiwa Adejobi, ya gabatar da wannan sanarwa ne ga daukacin jama’ar Kasa, bisa umarnin babban Sifetan ‘yan sandan na Kasa, Usman Baba.
Babu shakka akwai wasu ababen da ya kamata a nazarce su daga kunshin wannan sanarwa.
- Yadda Hare-Haren ‘Yan Bindiga Suka Shafi Rayuwar Al’umma A Kagara – Rahoto
- Na Koma Sayar Da Dankalin Turawa Ne Sakamakon Yajin Aikin ASUU – Malamar Jami’ar Oyo
Ma’ana, jama’a na da damar tofa nasu albarkacin baki game da wannan sabon umarni da ya gangaro daga Hedikwatar ‘yan sandan ta Kasa, a karshen wannan Wata da muke ciki na Yuli (July, 2022).
Matashiyar sanarwar na cewa;
“IGP Orders Arrest, Prosecution Of Skit, Movies Markers Over Use Of Police Uniform”.
“IGP Baba Issues Strong Warning On Portrayal Of Police In Films, Skits”.
Wadannan matashiyoyi biyu da aka gabatar a sama, sun kasance sune shimfidar da aka aza sanarwar hukumar a bisanta, babbancin turanci da aka samu, bai zamo ba face bambancin majiyoyin yada labarai da su ka naqalto sanarwar, amma duka suna nufin abu guda ne. Ga fassarar matashiyar; “Babban Sifetan ‘yan sanda Na Kasa Ya Ba Da Umarnin Kame Tare Da Tuhumar Masu Shirya Fina-finai Da Kuma Masu Shirya Wasannin Kakaci Bisa Amfani Da Kayan Jami’an Tsaro Na ‘yan sanda” “Babban Sifetan ‘yan sanda Na Kasa Ya Ja Kunne Game Da Nuna ‘yan sanda Da A Ke Yi A Fina-finai Da Kuma Wasannin Kakaci Da A Ke Shiryawa”.
Sanarwar hukumar ta ‘yan sanda, ta cigaba da nuna rashin jin-dadinta game da irin yadda za a ga masu shirya finafinai da kuma masu shirya wasannin kakaci ke amfani da kayan ‘yan sanda sasakai, ba tare da an sahale musu yin amfani da su ba.
Bugu da kari, hukumar, ta koka da irin yadda ake kan sayar da irin kayan jami’an tsaron na ‘yan sanda barkatai a cikin shaguna da kantuna ba tare da samun sahalewa daga wajen hukumar ‘yan sandan ta Kasa ba.
Ba ya ga masu shirya fim da masu wasannin kakaci, hukumar ma ta yi Allah-wadai da irin yadda za a ga hatta wasu daidaikun mutane na mallakar irin kayan na ‘yan sanda ba bisa ka’ida ba.
Kenan, abinda hukumar ta ‘yan sanda ke fadi shi ne, ashe wasu kayan Sarki da muke yawan gani a na amfani da su cikin fina-finai wadanda su ka hada har da bindigu, ba duka ba ne cikinsu ke samun sahalewar hukumar wajen amfani da su! Sannan, hukumar na son fada mana cewa, ashe da daman wuraren da ake ganin kakin ‘yan sanda na siyarwa, babu hannun hukuma ciki, wajen tafiyar da harkokin kasuwancin nasu.
Tun da ba mu na magana ba ne game da tsaron Kasa ba yanzu, za mu tafi kai-tsaye ne cikin tsokacin namu game da waccan sanarwa ta hukumar ‘yan sanda.
Hukumar ‘yan sanda Na Kyamar A Nuna Mugun Dan Sanda Cikin FinaFinai Da Wasannin Kakaci Cikin dai waccan sanarwa, hukumar ta ‘yan sanda, ta nuna rashin jin-dadinta irin yadda ake nuna ga wani mutum sanye da kayan ‘yan sanda ya fito a matsayin mugu maras tarbiyya a cikin fina-finai da sauran wasannin barkwanci da ake gabatarwa al’ummar gari, alhali ba a samu sahalewar hukumar ba wajen yin amfani da wadancan kaya nata da sauran kayan aiki na ‘yan sanda da za a ga a na amfani da su.
Bugu da kari, hukumar ta ‘yan sandan ta nuna cewa, aikata hakan ya sa6awa wasu tanadetanaden sadarorin dokar Kasa.
Hukumar ta ‘yan sanda ta yi jankunnen cewa, muddin masu shirya fina-fina da masu wasannin kakaci ba su daina nuna wani mutum cikin finafinansu sanye da kayan ‘yan sanda yana tsula-tsiyarsa, za su fuskanci fushi da kuma hukuncin shari’a.
Kwan-Gaba Kwan-Baya Daga Hukumar ‘Yan Sandan Cikin turancin da hukumar ‘yan sanda ta yi game da nuna mutum masharranci cikin fim ko wani wasan kakaci sanye da kayan sarki akwai harshen-damo a ciki.
Saboda, cikin sashen waccan takardar sanarwa ta folisawan, wani waje, sai a ga tamkar hukumar ta yarda a nuna mutumin banza sanye da kayanta a fim ko wasan kakaci, da sharadin an sami izinin yin hakan ne daga gare ta; “… Film makers or skit makers who portray the Nigerian Police Force Officers in a bad light, without applying for and being duly issued a permit letter for such portrayals, to desist with immediate effect or face the full wrath of the law…”
Cikin wancan turanci duka-duka za a ga cewa ya kunshi abubuwa biyu ne zuwa uku. Ga su kamar haka;
1- Ba a ce an hana nuna dan sanda a fim ko cikin wani wasan kakaci cikin mummunar sifa ba, sai dai, duk mai sha’awar yin irin wancan mummunan nuni na jami’an na ‘yan sanda, lalle-lalle ne ya nemi izini daga hukumar. Sannan, ya kar6i rubutaccen izini a matsayin hujjar sahalewa.
2- Duk masu nuna jami’an na ‘yan sanda cikin mummunar sifa a cikin fim ko wasan kakaci, ko dai su daina daga lokacin da su ka ji wannan sanarwa, ko kuma su hadu da fushin kotu.