Shafin Taskira shafi ne da yake zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu. Tsokacinmu na yau zai yi magana ne akan mata masu tsallaka Titi musamman ‘yan mata, duba da sakon da muka ci karo da shi cikin wannan shafi, inda wani bawan Allah ya bukaci da a yi magana akai, tare da boye sunanshi.
Sakon ya fara da cewa; “Ina so a yi magana a kan mata musamman ‘Yan mata ko na ce ‘yan gayu wadanda idan sun zo tsallaka Titi suke yanga, domin wani lokacin ma sai me abin hawa ya kauce musu ko ya tsaya, sabida idan za su tsallaka titi kamar wacce za ta shiga daki ko za ta je wajen sahibinta wajen yanga ba sa tunanin wannan abin hawan zai iya yi musu illah suna ganinsu Ajebotas ne”.
Dalilin hakan ya sa wannan shafi jin ta bakin wasu daga cikin mabiyansa game da wannan batu; Ko me za a ce a kan hakan? Wadanne abubuwa ne ya kamata me tsallaka Titi ya yi musamman budurwa?
Ga dai bayanan nasu kamar haka: Sunana Comr, Nr. Ibrahim Lawan Stk:
Tabbas hakan ba wai sabon abu bane ba kuma ba yau aka fara ba, sannan ba mu san lokacin dainawarsa ba a gurin masu aikatawa ba, saboda abu ne wanda wasu ya zama jikinsu, wasu ma sun maida abin kamar wayewa, sai dai ni a ganina ma ko in ce a ra’ayina rashin wayewa ne rashin sanin ya kamata ne, da kuma rashin sanin dalilin da ya sa Allah ya bawa mutum rayuwa da lafiya, hakan ya sa wasu suke aikata hakan. Dole ne mutum ya kasance mai nutsuwa da lura, tare da kallon kowane bangare na tituna domin kaucewa hadarin abin hawa, kaucewa amfani da waya ta hanyar yin kira ko kasancewa a manhajar kafofin sadarwa na zamani, kaucewa yin zance tare da abokan tafiya, saka kaya wanda ba za su matse mutum ba domin kaucewa faduwa yayin tsallaka titi da gudu, saka takalmin da ba zai sa santsi ya kwashi mutum ba ko kada mutum ba, tsallaka kwalta da gudu domin kaucewa abin hawa masu gudu tare da tsautsayi daka iya faruwa, bin dokokin tsallaka kwalta.
Shawarta ga masu wannan dabi’ar ita ce; ya kamata su san cewa rayuwar su da lafiyar su nada matukar mahimmanci musamman a halin da ake ciki na tsadar rayuwa inda wasu kan yi amfani da lafiyar domin nemawa kai mafuta, wanda a yanzu duk wanda aka taba da abin hawa an cuce shi ba yadda zai yi ko za ta yi, sannan su kiyaye aikata hakan domin kaucewa yanayin fadawa hadari da ka iya taba lafiyar su ko ma rayuwar su gabadaya, sannan su bi duk wata doka ta tsallaka titi yadda ya kamata.
Sunana Zaynab Muhammad Maijama’a Daga Jihar Kano:
To tsallaka titi dai ba waje bane na yanga, ko iyayi, ko nuna Isa, ko wani salo da sauransu, wani lokacin za ka ga mutum zai tsallaka titi amma yana ta faman yanga kamar an yi masa dole, musamman ma mu ‘Yan Mata, kuma hakan ba daidai bane, hakan hadari ne ga lafiya da kuma rayuwa. A lokacin tsallaka titi ya kamata mu ajiye duk wata yanga da iyayi da wani salon tukunna, in ya so bayan mun tsallaka sai mu cigaba, tunda hakan ya zama kamar jinin jikin mu ne mu Mata, kada garin neman gira a rasa Ido, ita lafiyar nan tattalata ake ana riritata, bai kamata ace dan ke ‘Yan mata ce kin yi kwalliya ko kuma kai gaye ne ajebota da sauransu don za a tsallaka titi sai an yi wani salo ko iyayi ko nuna Isa ba, domin shi tsautsayi ba ruwanshi da duk wannan gayun da salon, mota idan ta buge ka ko ta bige ki ke ce ki ka cutu, wata kila ma ya zamo an nakasa, ko jinya, bare yadda lafiya take tsada a yanzu, to gaskiya ya kamata mu cire duk wani yanga da sauran abubuwa makamancin haka,in mun zo tsallaka titi. Shawarata ga masu tsallaka titi yadda suka ga dama shi ne, titi dai ba waje ne na yanga ko kuma salo ba, domin ita lafiya da rayuwa ba’abar wasa ba ce, ya kamata idan ka zo tsallaka titi ka maida hankali wajen lura da kuma kiyayewa, kayi abin da ya kamata, in yaso koma mene ne bayan ka tsallaka ka wuce sai ka ci gaba da yi.
Sunana Nura Garba Dutse A Jihar Jigawa:
Akwai takaici matuka da gaske ace za ka tsallaka titi amma kana tafiya kana jan aji ko yanga ga wasu ‘yan mata ko samari ‘yan gayu, akwai bukatar lallai a dunga tsawatar musu duk lokacin da aka gansu ko aka ji suna aikata hakan domin wataran za a ji labarin da ba a son ji kwarai. Abin da ya kamata duk wani mai tsallaka titi yayi shi ne, nutsuwa kafin ya fara dubu tahowar ababen hawa, da kuma nisansu kafin su karaso wajensa, ya tabbatar idan babu nisa kar ya tsallaka idan da nisa shi ne zai tsallaka shi ma da sauri saboda titi ba gida bane balle unguwa shi ne nutsuwa kafin ya fara dubu tahowar ababen hawa, da kuma nisansu kafin su karaso wajensa, ya tabbatar idan babu nisa kar ya tsallaka idan da nisa shi ne zai tsallaka shi ma da sauri saboda titi ba gida bane balle unguwa ko kuma wata hanya da ababen hawa ke tafiya a hankali, kula da Lafiya ya fi zarya zuwa wajen likita. Shawara ta a garesu lallai su sani duk wani abu ko na kyau ko na kyakyali sai da rai da lafiya aka yi, lallai su kula da lafiyar su ta hanyar taka tsantsan da duk wani abu da zai taba lafiyarsu domin duk ranar da aka bigesu a mashin ko mota wanda suke don shi ko takansu ba zai yi ba.
Sunana Hafsat Sa’eed Daga Neja:
Gaskiya hakan bai dace ba sabida titi ba abun wasa bane, idan wani ya kauce maka wani zai iya zuwa ba tare da ya kula da kai ba ya buge ka Allah ya kiyaye, musamman idan ya taho da abun hawan a guje, wannan yangar a barta a ajjiye ta bayan an tsallaka a dauka a ci gaba da yi.
Sunana Aminu Adamu Malam Maduri A Jahar Jigawa:
Tabbas wannan matsala ta yanga ko iyayi da wasu mata ke yi a lokacin tsallaka titi akwai abun takaici, duba yadda titunan suke da hadari, domin akwai masu tukin ganganci dama kuma ‘yan koyo wanda a lokuta da dama ba sa tafiya a hankali. To magana ta gaskiya abun da ya kamata mutum yayi lokacin tsallaka titi shi ne ya tattara hankalinsa guri daya domin ya duba kowane bangare na titun sannan kuma ya hanzarta wajen tsallakawa ba wai ya tsaya yanga ko kuma wasa ba, domin kaucewa jefa rayuwa cikin hadari, domin da yawan masu abubuwan hawa a yanzu suna tuki suna tunanin duniya ba wai kai ne a gaban su ba. To shawarata a nan ita ce lafiya dai abar kulawa ce don haka bai dace ba mutum yayi wasarere ko kantafi da ruyawar sa, domin ko ba mutuwa ba akwai nakasawa wanda ba wanda yake sonta, don haka sai ana yin hanzari da kuma takatsantsan wajen tsallaka titi ba wai yanga ba ko wasa, su kuma direbobi ya kamata su ma suke tafiya a hankali musamman idan sun shigo gari wajen dake da tarin jama’a ko kuma wajen da danja take ko sha tale-tale domin kaucewa afkuwar hadari, daga karshe nake addu’ar Allah ya kare mu gabadaya don alfarmar Annabin rahama (S.A.W).
Sunana Aisha T. Bello Daga Jihar Kaduna:
A gaskiya mata masu yanga in sun zo tsallaka titi, abin takaici ne. Sai ka ga suna tafiya kamar masu shiga daki ko kuma sun sayi titin. Irin haka na haddasa hatsari musamman akan titunan manyan birane da aka gyara. Wasu masu motocin basu tafiya a hankali, yayin da aka zo irin wannan tsallakar titin ana nawa, da wuya mai mota yayi ‘controlling’ abun hawa yayin da yake gudu. Ya kamata mutum, musamman ‘yan mata su duba titi da kyau, yayin tsallakawa. A tsallaka da hanzari lokacin dake da tazara tsakanin su da motoci. A sani ba burgewa bace yanga kan titi, rai dai daya ne daga inda ya kufce kuma shi kenan.
Sunana Yahaya Adamu Aliyu, Dala Jihar Kano:
To magana ta gaskiaya ni idan haka ya faru da ni ina tafiya, zan kwada mata mari ko na kara mata gudu. Ya kamata idan za ka tsallaka titi ka/ki fara tattara hankalinka a guri daya sannan ka duba kowane bangare la’akari da yawan motoci daidai da dacewar tsallakawa a hankali ko da sauri koma da gudu. Su daina su sani cewa a addinance duk wanda ya kashe kansa da ganganci wuta zai shiga kai tsaye idan kuma ya ji ciwo ko wane iri ya sani dole sai yayi ibada akowane yanayi yake, kin yin hakan kuma laifi ne babba a gurin ubangiji.
Sunana Sadiya Abubakar Maru (Yar Gatan Royal) Garin Gombe:
Tabbas ba zai yu ki yi gudu a kan titi ba, amma fa ki sani Titi ba dakinki bane, sannan ba tsakar gidanku bane, tsakiyar titi kuma bai kama wajen yanga ba, don bakin rijiya ba wajen wasan yaro bane, dole ne ki lura da yadda za ki tsallaka titi gudun abun da zai je ya dawo. Kowanne da bangarensu, su ma masu abun hawan akwai nasu, musamman matasa wasu gudunsu ba ya tashi sai sun ga an zo dab za a hadu sai su kara kaman za su yi kan mutum wani har ma ya firgitaka, amma hakan ai yana da magani don warwaro daya baya kara. Ki fahimci wani irin waje ki ke, ko shi kanshi yanayin titin da za ki tsallaka din, shin mai yawan jama’a ne? Ko akasin haka? Duba gefe da gefenki yayin tsallaka titi sai ki nutsu da tafiyarki, ba gudu ba yanga don ki ka yi yanga tabbas za ki ga yanga. Muddin kin san za ki tsallaka titi musamman titi mai cinkoso da yawan masu ababen hawa lallai ne ki lura da yanayin kayan jikinki (Dinkinki) da kuma takalman dake kafarki, (Masu tsini) ku lura da wadannan abubuwan, ki sani idan wani ya kadeki ya tsaya wallahi wani gaba zai yi ba ma zai bi ta kanki ba to ina amfanin badi ba rai? Hanyar lafiya a bita da shekara, ko yaya ne lafiya ai jari ce. Da ki je a kadeki gwara kin hakura da yangarki na sekonni ki tsallaka Titi lafiya kalau. Allah ya dada kare mu da kariyar sa.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary) Jihar Kano Rano:
Rashin sanin ciwon kai da jiki mana domin ran nan guda daya kowa yake da shi, sannan ita kuma lafiyar nan ririrtata ake yi yanzu. Nutsuwa sannan duk wani sauri a ajiyeshi a gefe mu jira ababawan hawa su ragu idan kuma ba a sami hakan ba mutum ya jira ya hango masu tafiya a hankali sannan idan mun tashi tsallakawa mu yi sauri mu wuce domin wasu masu tuka ababan hawan a lokacin ma ‘maybe’ suna can suna wani tunanin ba lallai a ce sun kula da masu tsallaka titi ba a wannan lokacin. Su daina wannan domin shurme ne yin hakan ba burgewa bane domin ko a cikin dabbobi wasu idan za su tsallaka titi a guje suke wucewa to ina ga mu mutane da Allah ya fifitamu a kansu?. Domin wallahi wasu masu tuka abin hawan ma koda sun kade ka ko ka rayu ko ka mutu ba lallai ace sun tsaya ba, kuma koda sun tsaya kai dai an cuce ka wasu ma koda babu mutuwa to za a iya samun wata tawayar da sai dai mutum ya mutu da wannan aibun.
Allah ya sa mu gyara amin.
Sunana Fatima Tanimu Ingawa Daga Jihar Katsina:
Shakka babu akwai mata da dama masu irin wannan dabi’ar, domin muna yawan gamuwa da irin su a wurare mabambamta. Shi fa titi hanya ce ta walwalar kai komon abun hawa amma ba na mai tafiya a kasa ba. Kai ko da hanya ce ta bi da kai shi ya sa ake son mutum ya rika bin gefe-gefe da lura. Wajen tsallakar titi kuwa an so mutum ya kiyaye ka’idojin da aka tanadar yayin tsallakar titi, wato a duba hagu da dama in an tabbatar babu wani abun hawa kusa sai a hanzarta tsallakewa cikin hanzari don a rabu da titin. Mata masu wadannan ganganci sai ma in ce wasa da rai ne don komai na iya faruwa dasu. Walau su hadu da mai garaje da ya riga ya kure ma gudunsa, ko kuma birki ko wani abu ya kwace masa abun da ake gudu ya auku.
Mafi a’ala shi ne don Allah su yi hakuri su daina, su san inda za su rika yin yauki da yangar su amma ba wurin da za su yi wasa da rai ba. Kowa dai rai yai wa dadi ai baran mai shi ne. Allah ya sa su gane su gyara.
Wassalamu Alaikum