Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, ta karɓi bashin Bankin Duniya dala biliyan ɗaya da rabi, bayan cika sharuɗɗan da bankin ya gindaya a kai.
Wasu daga cikin tsare-tsaren da bankin duniya ya buƙaci gwamnatin Nijeriya ta aiwatar don samun bashin sun haɗa da cire tallafin man fetur da sauya dokar haraji wanda kawo yanzu tana gaban majalisar dokoki don neman sahalewarta.
- Bankin Zenith Ya Tallafa Wa Matasa Da Naira Miliyan 77 A Jihar Legas
- Bankin Duniya Ya Bukaci A Kare Kasashe 26 Daga Fadawa Talauci A 2050
Wani rahoton gidan talabijin na ‘Channels TV’ ya bayyana cewa, bashin da Nijeriya, ta samu kashi biyu ne na jimillar dala biliyan 1.5 don gyaran tattalin arziki (Reforms for Economic Stabilization to Enable Transformation) da kuma dala miliyan 750 don ayyukan ci gaba (Development Policy Financing Program).
Wata takarda da bankin ya fitar ya nuna cewa an raba bashin ne gida biyu zuwa miliyan 750 kowanne, wanda tun a ranar 2 ga watan Yulin 2024, gwamnatin Nijeriya ta kaɓi kason farko, daga baya kuma aka bayar da kaso na biyu a watan Nuwamba bayan cika sauran sharuɗɗan aiwatar da tsare-tsaren tattalin arzikin da gwamnatin ta Bola Tinubu ke yi a yanzu.