Gwamnatin Jihar Kwara ta sake kama Mabarata 40 da suke gararamba a titunan Ilorin, babban birnin jihar, a wani yunƙuri na daƙile aiyukan bara da kare martabar jama’a. Hakan ya biyo bayan haɗin gwuiwar jami’an Ma’aikatar Walwala Da Ci gaban Jama’a da Hukumar Gyaran Hali ta Nijeriya (NCS), reshen jihar Kwara. Wuraren da aka yi kamen sun haɗa da: Tipper Garage, Offa Garage da Garin Alimi.
A yayin binciken da aka yi, jami’an tsaro sun gano dalar Amurka a wajen wani Musa Mahmuda daga Jihar Kano, yayin da aka kama wani da wuƙa a hannunsa.
Rahotanni sun ce daga cikin waɗanda suka aka kamo, bakwai an taɓa kama su da laifin bara a baya amma suka sake komawa tituna duk da gargaɗin gwamnati. Wannan ya nuna yadda ’yan bara ke ƙoƙarin kauce wa kamawa sana’ar ta hanyar sauya wuraren zama.
- An Kaddamar Da Tashar Watsa Labarai Ta CMG A Chengdu
- Sin Ta Samu Karuwar Kaso 9.9 Na Sabbin Kamfanoni Masu Jarin Waje A Bara
Kwamishiniyar Walwala da Ci gaban Jama’a, Dokta Mariam Imam, ta bayyana cewa shirin na gwamnatin jihar na kawo ƙarshen bara yana samun nasara, tana mai cewa adadin waɗanda aka kora ya ragu daga 94 a baya zuwa 40 a wannan karo. Ta bukaci jama’a da su daina bayar da sadaka kai tsaye ga masu sana’ar bara, su maida taimakonsu ga marayu da cibiyoyin addini.
A nasa jawabin, wakilan NCS, Adebayo Okunola, ya ce za a ɗauki matakan ladabtarwa a kan waɗanda aka kama domin su zama izina ga sauran masu niyyar komawa bara. Ya bayyana cewa, “Za mu tabbatar sun tsaftace tituna, ta hanyar sa su yin shara domin su gane cewa akwai mutunci a aikin halal.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp