Shugabancin jam’iyyar PDP na kasa ya janye dakatarwar da aka yi wa tsohon gwamnan Jihar Katsina Ibrahim Shema da tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose da Sanata Pius Anyim da Farfesa Dennis Ityavyar da Dikta Aslam Aliyu.
Har ila yau, ta janye dakatarwar da ta yi wa Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benue na gurfana da shi a gaban kwamitin ladabtarwa bisa zargin cin zarafin jam’iyya.
- Zaɓaɓɓen Gwamnan Kano Ya Naɗa Sakataren Yaɗa Labarunsa
- Majalisa Ta Yi Taron Jin Ra’ayoyin Jama’a Kan Kudirin Dokar Kafa Hukumar Kula Da Almajirai
Sakataren yada labaran PDP na kasa, Debo Ologunagba, ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis bayan wani taron kwamitin zartaswa na jam’iyyar a Abuja.
Ya kuma bayyana cewa jam’iyyar a shirye take don ganin an sasanta tsakanin mambobinta.
Ya ce, “Kwamitin zartaswa na kasa na jam’iyyar PDP a taronta na yau, Alhamis, 30 ga watan Maris, 2023 ya tattauna sosai kan abubuwan da suka faru a jam’iyyar.
“Kwamitin ya amince da yin sulhu tsakanin shugabannin jam’iyya da masu ruwa da tsaki don samar da jam’iyya mai hadin kai don ci moriyar mambobinmu da ‘yan Nijeriya baki daya.
“Sakamakon abin da ya faru shi ne an sauya matakin da Gwamnan Jihar Benue, Samuel Ortom ya yi wa kwamitin ladabtarwa na kasa.
“Kwamitin a cikin wannan yanayin ta sauya dakatarwar da aka yi wa mambobin babbar jam’iyyarmu.
“Dole ne jam’iyyar PDP ta mai da hankali yayin da muke ci gaba da daukar dukkan matakan da suka dace na kwato hakki dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, da aka kwace a ranar Asabar 25 ga Fabrairu, 2023, a kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa.”
Idan za a tuna cewa jam’iyyar PDP ta dakatar da shugabannin jam’iyyar biyar a karkashin jagorancin shuganacin Iyorchia Ayu.
Sai dai sabon shugaban rikon kwarya na jam’iyyar PDP, Aliyu Madagum ya jagoranci yin sulhu a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar.