Bayan hukuncin da kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta yi a ranar Litinin da ta gabata, inda ta tabbatar wa Arc Shehu Tukur da nasara, dan takarar kujerar Sanata a mazaber Nasarawa ta yamma, Barista Labaran Shuaibu Magaji ya yi kira ga ilahirin magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu.
Ya ce ko kadan ka da kowa ya tayar da hankalinsa domin shari’a ta yi hukunci da bai yi masu dadi ba. Ya ce su ci gaba da addu’a domin ya tabbata za su yi nasara nan gaba.
- Umarnin Kotu: Gwamnatin Kano Ta Kulle Masallatai Da Makarantar Abduljabbar Kabara
- Shugaban Kasar Equatorial Guinea: Kasashen Yamma Sun Yayata Furucin Wai “Sin Na Kafa Tarkon Bashi” A Yunkurin Su Na Dakile Kasar
Labaran Magaji ya bayyana haka ne ga manema labarai bayan yanki hukunci ta yanar gizo da kotun daukaka kara ta yi a ranar Litinin.
Kotun mai dauke da alkalai uku, Mai shari’a Muhammad Danjuma da B.Georgewili da Ibrahim Jauro sun kalubalanci hukuncin da Mai shari’a Nahezina Afolabi mai sauraron karar zabe a kotun gwamnatin tarayya da ke zamanta a Lafia ta yi ranar 2 ga watan Nawambar 2022, inda ta bukaci Jam’iyyar APC da ta sake gudanar da sabon zabe cikin sati biyu a mazabar Nasarawa ta yamma.
Mai shari’a Nahezina Afolabi ta ce ta sauke zaben ne saboda ta samu gamsassun hujjojin da suka tabbatar da an sauya masu zaben fid da gwani na Sanata da ya gudan ranar 4 ga watan Junin 2022.