Wasu ‘yan bindiga wadanda ake kyautata zaton cewa masu garkuwa ne, sun kashe wani dalibi mai suna Abdulmalik Tukur, da ya kamala karatunsa a jami’ar Modibbo Adama (MAU), da ke Yola jihar Adamawa bayan sun karbi kudin fansa naira dubu dari biyar.
Majiyarmu wadda ke kusa da iyalin ta bayyana mana, mamacin bai dade da kamala bautar kasa ba a bana, nasu garkuwa sun tafi da shi tare da wasu mutane.
- Kungiyar Kawance Ta Sin Da Niger Na Goyon Bayan Manufar Sin Daya Tak
- Kungiyar Kawance Ta Sin Da Niger Na Goyon Bayan Manufar Sin Daya
Dalibin mai kimanin shekara 32, kwanan nan ya kamamla bautar kasa a jihar Filato, a kan hanyarsa ta dawo wa gida, mau garkuwan suka kama shi tare da wasu mutum shida.
Dukkan wadanda aka kama su tare, an sake su bayan sun biya kudin fansa naira dubu dari hudu kowannensu, amma shi Tukur sai suka ce, sai an kawo naira dubu dari biyar.
Bayan an dade ana tattauna wa, sai suka daidaita akan za a ba su naira dubu dari biyar, a matsayin kudin fansa.
Ya ce, an dauki kudin an kai wa masu garkuwar a daji.
Bayan sun karbi kudin sun nuna musu wanda suka yi garkuwar da shi, sai suka mika musu, suka ce, ga shi nan su tafi da shi, ba yan sun juya za su tafi, sai suka harbe shi da bindiga, nan take ya fadi ya mutu.
Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar Adamawa SP Sulaiman Nguroje, har zuwa lokacin hada wannan labara, ya ce, bai samu wani bayani a kan wannan labara ba.