Bayan Komawar ‘Yan Wasan Argentina Gida, Gwamnatin Kasar Ta Ayyana Hutu A Kasar
BBC ta rawaito cewa bayan zakarun gasar cin kofin duniya, Argentina sun isa filin jirgin sama na Buenos Aires inda dubban jama’a suka fito domin yi musu maraba.
- Qatar 2022: Faransa Ta Sha Kashi A Hannun Argentina Inda Ta Yi Nasarar Cin Kofin Duniya
- Qatar 2022: Argentina Ta Je Matakin Wasan Karshe
Gwamnatin kasar ta ayyana ranar Talata a matsayin ranar hutu domin gudanar da bukukuwa.
Magoya bayan kasar sun yi jerin gwano a kan titunan kasar domin yi musu maraba.
Nan gaba a ranar Talata ne za a gudanar da babban biki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp