Argentina ta je matakin wasan karshe na Gasar Cin Kofin Duniya bayan doke Croatia da ci 3 babu ko daya.
‘Yan wasan Argentina, Messi da Alvarez ne suka jefa mata kwallo a raga.
- An Tsaurara Matakan Tsaro A Abuja Saboda Bukukuwan Karshen Shekara
- Sin Ta Fitar Da Rukunin Farko Na Hotunan Da Aka Dauka Da Na’urar Binciken Rana Ta Kuafu-1
Kawo yanzu Messi ya zura kwallo ta shida a gasar, sannan kwallo ta 11 a tarihin gasar cin kofin duniya da ya taba bugawa.
Talla
Argentina dai za ta kara da daya daga cikin wanda ya fito tsakanin Faransa da Morocco, wadanda za su kara a daren ranar Laraba.
Ita kuwa Croatia za ta jira kasar da ta yi rashin nasara a tsakanin Faransa da Morocco don buga wasan neman mataki na uku na gasar.
Talla