Ministan yaɗa labarai da wayar da kai, Alhaji Muhammad Idris ya bayyana cewa nasarar da Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya samu a kotun ƙoli za ta ƙara masa himma wajen ci gaba da gudanar da ayyukan gina nagartacciyar ƙasa.
Ministan ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ya gabatar dangane da hukuncin da kotun ta yanke.
- Tsohon Firaministan kasar Sin Li Keqiang Ya Rasu
- Tsarin Canji Na Bai-daya Hanya Ce Ta Tsaftace Kasuwar Shinku
Tun farko, Ministan cewa ya yi maraba da bakin da suka halarci taron, wanda ya ce, an shirya ne bayan hukuncin shari’ar da Kotun Ƙoli ta yanke na tabbatar da Nasarar Tinubu. Hakan ya kawo ƙarshen ƙorafe-ƙorafen ƙararrakin da aka riƙa shigarwa a kotuna game da nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ya ƙara da cewa “maganar shari’ar zaɓen Shugaban Ƙasa ta kare, yanzu lokaci ne da za mu tunkari aikin tafiyar da gwamnati ba tare da wani abu ya ɗauke mana hankali ba.
“Tabbas wannan babban ƙalubale ne, musamman a wannan lokaci da tattalin arziki ke fuskantar mawuyacin hali, ba a Nijeriya kaɗai ba, har duniya baki ɗaya.
“Saboda haka, tilas a taru mu haɗa hannu wuri ɗaya, domin magance wannan ƙalubale da ke tunkarar mu. Shugaba Tinubu ya bayyana a fili cewa shi Shugaban Ƙasa ne na kowane ɗan Nijeriya, ba tare da bambancin yanki, ƙabila, siyasa ko addini ba.”
Minista Idris ya ce, tun bayan hawansa mulki a ranar 29 ga Mayu, Shugaba Tinubu ya na ta aiki tuƙuru wajen ƙoƙarin samun nasarar Ajandar Farfaɗo da Nijeriya, wadda ta na daga cikin dalilan sa na kishin zama shugaban ƙasa.
Ya aiwatar da manyan tsare-tsare, duk da tsaurin da tsarin ya fuskanta amma tsaurin na wani taƙaitaccen lokaci ne. Kuma ta haka ne aka gina tubalin girka ƙasaitaccen tattalin arziki, samar da yalwar da kowane ɗan Nijeriya ya cancanci ya samu.
Game da cire tallafin man fetur, Ministan cewa ya yi “Kamar yadda ku ka sani, cire tallafin fetur abu ne da ya samo tushe daga Dokar Fetur ta 2021, wadda yanzu ta ke ƙara tanadar wa Gwamnatin Tarayya da Jihohi maƙudan kuɗaɗen da za su riƙa yin ayyukan inganta rayuwa da bunƙasa ƙasa.”
Game da halin ƙunci da ake ciki a ƙasar nan, Minista Idris ya ce “Babu gwamnatin da ta san abin da ta ke yi da za ta jefa al’ummar ta cikin halin ƙunci da gangan. Shi ya sa mu ke jaddada cewa wannan hali da ake ciki zai wuce cikin taƙaitaccen lokaci nan gaba. Daga nan sai mu shiga yanayin yalwa mai dorewa.”
Ya kuma ce, Gwamnatin Tinubu na ɗaukar dukkan matakan da su ka wajaba domin sauƙaƙe wa talakawa raɗaɗin tsadar rayuwar da su ke fama da ita a yanzu.
Ya bayyana cewa, “Daga cikin hanyoyin akwai: Ƙarin Naira 35,000 kan albashin ma’aikata, har tsawon watanni shida a jere. Kafa Asusun Gina Ayyukan Raya Ƙasa na Jihohi. Ƙaddamar da sayen motoci masu aiki da gas, domin sauƙaƙa tsadar zirga-zirgar motoci.”
Idris ya bayyana cewa “nan da 2024 za a fara shirin bai wa ɗalibai rance.”
Ya ce ana kan aikin tsare-tsaren Kasafin Kuɗi na 2024. “Saboda haka ‘yan Nijeriya su kwantar da hankalin su. Wannan kasafin kuɗin na farko na Gwamnatin Tinubu zai kasance na farko wanda kacokam ya maida hankali kan samar da bunƙasar tattalin arziki da samun yalwa ga kowa da kowa.
Ya ƙara da cewa “Ina ƙara yin kira ga ‘yan Nijeriya da mu ci gaba da haƙuri, ƙasar nan za ta warware, ta bunƙasa ba da daɗewa ba. Mu na fatan samun ƙasaitacciyar ƙasar da kowa zai amfana da cin moriyar bunƙasar ta.”
A ƙarshe, Ministan ya kara nananta ikirarin Tinubu bayan da kotun koli ta tabbatar da Nasararsa, “Ajandar Farfaɗo da Nijeriya zuwa ƙasaitacciyar ƙasa ta ƙara samun karsashi. Zan ci gaba da yin aiki ba dare ba rana domin gina ƙasar da ta cancanci nagartattun mutane irin ɗaukacin mu baki ɗaya ke fatan samu.”