Tsohon ministan harkokin Neja Delta, Godsday Orubebe, ya koma jam’iyyar APC mai mulki, shekaru bakwai bayan da ya yi yunkurin dakile nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin shugaban Nijeriya.
LEADERSHIP ta samu rahoton cewa Buhari na shirin karbar Orubebe cikin jam’iyya mai mulki nan da ‘yan kwanaki masu zuwa.
Orubebe mai biyayya ne ga jam’iyyar PDP da kuma shugaban kasa Goodluck Jonathan, a ranar 31 ga Maris, 2015, yayin da yayi yunkurin kawo cikas a wurin tattara sakamakon zabe na Shugaban kasa wanda hukumar zabe ta kasa INEC ke gudanarwa a Abuja.
An nada Orubebe a matsayin minista na musamman a ranar 6 ga Afrilu, 2010, lokacin da Jonathan ya kafa sabuwar majalisarsa a matsayin mukaddashin shugaban kasa.
A matsayinsa na wakilin Jonathan a wurin tattara kuri’u, ya zargi shugaban INEC na lokacin, Farfesa Attahiru Jega, da hada baki da babbar jam’iyyar adawa ta APC a wancan lokacin. Amma daga baya ya nemi gafarar al’ummar kasar kan lamarin, inda ya kara da cewa ya yi nadamar aikata wannan halin.