Rundunar ƴansandan jihar Borno ta tabbatar da kuɓutar wasu ƙananan yara biyu, Ayuba Ishaku mai shekaru 12 da Yakubu Haruna mai shekaru 13, daga hannun ƴan ta’addan Boko Haram, bayan sun shafe kusan shekaru shida a tsare. An sace su ne tun suna da shekaru 6 da 7 a ƙauyen Mandaragrau da ke ƙaramar hukumar Biu, a ranar 29 ga Disamba, 2019.
A cewar jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴansanda, ASP Nahum Daso, yaran sun bayyana a ofishin ƴansanda da kansu a ranar 12 ga Yuli da misalin ƙarfe 5:30 na yamma, inda suka ba da cikakken bayani kan yadda aka sace su da yadda suka tsere. Sun bayyana cewa an sace su tare da iyayensu, amma ƴan ta’addan sun bar iyayen a hanya saboda rashin ƙarfi.
- Sojoji Sun Kai Hari Maɓoyar Boko Haram A Borno, Sun Kashe Wasu ‘Yan Ta’adda
- Sojoji Sun Kai Hari Maɓoyar Boko Haram A Borno, Sun Kashe Wasu ‘Yan Ta’adda
Sun ce ƴan ta’addan sun kai su wani sansani a yankin Mangari, Tumbun Mota a Baga, inda aka ci gaba da amfani da su a matsayin yan aikin gida da kuma horar da su kula da makamai. An ce maza bakwai da aka sace tare da su an koyar da su yaki tare da ISWAP, amma yaran ba a bar su shiga faɗa ba.
Yaran sun ce sun shafe watanni suna shirya tserewa cikin sirri, inda suka samu dama a ranar 10 ga Yuli lokacin da mafi yawan mayakan suka fita aiki. Bayan tserewarsu, sun yi tafiya a ƙafa ta cikin daji har suka isa Maiduguri da misalin ƙarfe 4:45 na yamma a ranar 12 ga Yuli.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp