Dan kasar Kazakhstan mai suna Ruslan Tulenov ya tuna cewa, a shekarar 2013 ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ambaci labarinsa a karo na farko, kuma a wancan lokacin, yana zaune ne a lardin Hainan na kasar Sin. Yanzu, shekaru 9 ke nan, kuma har yanzu, shugaba Xi bai manta shi ba, ya iya tuna labarinsa.
Ya kara da cewa, a baya, na kan yi tunanin cewa, shugabanni suna nesa da mu, da kyar a hadu da su. Amma, yanzu, yana ganin, shugaba Xi ba shi da nisa da mu, kuma yana da ra’ayoyi da dama wadanda suka dace da zamani, ina ganin shi shugaba ne mai hikima. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp