A ranar Juma’ar da ta gabata ne shugaba Bola Tinubu ya kammala ziyarar aiki da ya kai birnin Paris na kasar Faransa, inda ya halarci taron koli kan lamuran da shuka shafi Kudade da hanyar rage basuka na Duniya, wanda shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya shirya.
Baya ga halartar taron da ya wakilci Nijeriya, Shugaba Tinubu ya kuma gudanar da manyan tarurrukan bayan fage tare da takwarorinsa shugabannin kasashe da gwamnatoci da shugabannin ‘Yan kasuwa na duniya da manyan shugabannin manyan cibiyoyin hada-hadar kudi da raya kasashe daga sassan duniya.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Dele Alake ya fitar, taron ya baiwa shugaban kasar damar yin hasashe da fadada tunani a fannin hada-hadar kudi, tabbatar da adalci ga nahiyar Afirka, a daidai lokacin da duniya ke kara azama a fannin wutar lantarki da kuma yadda kasashen duniya ke kara samun ci gaba a fannin makamashi dama yin gaggawar magance matsalolin talauci da sauyin yanayi.
Shugaba Tinubu, wanda tun da farko an shirya zai dawo Abuja ranar Asabar, yanzu zai wuce birnin Landan na kasar Birtaniya domin wata gajeriyar ziyara ta musanman da zai gabatar.
Shugaban zai dawo kasar nan da dan lokaci don gudanar da bukukuwan Sallah mai zuwa.