Fitowar dunkulen jini yayin jinin al’ada (blood clots), ba matsala ba ne ko kadan; yanayin halittar jinin al’adarki ne.
Wasu matan, su kan fitar da irin wannan dunkulen jini ko da sau daya ne tak a rayuwarsu, wasu kuma wani watan su fitar; wani kuma su ga babu.
- Kamfani Ya Maka Bankin Globus A Kotu A Kan Karya Yarjejeniyar Bashi
- Lallai A Hukunta Waɗanda Suka Kai Mamaya Ofishin NLC – TUC
Har ila yau, abin da ke kawo wannan matsala shi ne; yayin da mace ke yin al’ada, sai murfin mahaifarta ya bude ta yadda jinin zai samu fita, kafin jinin ya fita daga jikinta; sai ya yi kauri sosai tare da yin yauki.
Lokacin al’ada, jiki ya kan rika fitar da shi da sauri ta yadda ba zai samu ya narkar da shi ba. Wani lokacin ma, zai mayar da jinin ya yi yauki ko kuma dan kauri. Sannan shi wannan dunkulallan jini, yana fitowa ne baki-baki ko kuma jajaja.
Saboda haka, babu wata damuwa idan aka ga ya zo a haka; domin kuwa za a iya samu wani watan watakila bai kai girman na wannan watan ba, ko kuma a ga kwata-kwata ma bai zo a wani watan ba.
Shawara a nan ita ce, mata masu irin wannan al’ada; maimakon su rika amfani da audigar mata (pads), ya fi kyau su nemi kofi (menstrual cup) a rika amfani da shi.
‘Menstrual cup’, wani kofi ne da mata ke amfani da shi maimakon audiga ko kunzugu (pads or tampons). Ana sa ko tara wannan kofi ne, yadda gudan jinin zai rika shiga cikin kofin kai tsaye, akwi kuma manya da kananansa.
Haka zalika, an yi wannan kofi ne; musamman domin wadanda suke zubar da jini da yawa, sannan ya danganta da kalar da mace za ta yi amfani da ita, ma’ana ya danganta da shekarunta.
Mata ‘yan kasa da shekara 30, na amfani da karami ne, wadanda suka wuce shekara 30, na amfani da babban; wadanda kuma ba su taba haihuwa ba, ko kuma sun taba amma ta hanyar yi musu tiyata (CS), sai su yi amfani da karamin su ma.
Haka nan kuma, ‘yan shekara talatin; idan sun taba haihuwa, suna kuma ci gaba da haihuwar da kansu; sai su yi amfani da babban.
Shi wannan kofi (menstural cup), akwai gajere; akwai kuma dogo. Suna yin wani da tauri, wani kuma suna yin sa da laushi.
Amma idan ana fitar da jinin da yawa, misali kamar duk bayan awa guda canza audiga (pad), ko idan kuma yana fitowa da yawa da girma kuma da tauri, sai a yi maza a garzaya zuwa asibiti; amma idan ba da yawa yake zuwa ba, sannan kuma yana daukar kamar awa biyu ko uku bai zo ba; wannan babu wata damuwa.
Idan dunkulen jinin ya zama mai duhu sosai da kuma tauri, wannan ba wata matsala ba ce, musamman idan ya canza daga ruwan kasa zuwa baki-baki, domin kuwa yana nuna cewa; jinin ya zo karshe kenan.
A karshe, idan aka lura cewa; dunkulen jinin yana fita da dama duk bayan dan lokaci, sannan jini na fita da da yawa a kowane wata, sai a garzaya zuwa asibiti don ganin likita.
Majiya: Dandalin Shawarwari
A Kan Lafiyarku