Kari (Fibroids), na da matukar hadari; wanda a halin yanzu mata da dama ke fama da shi; manyansu da kuma ‘yan mata. Kazalika, ya kan yi sanadiyyar hana wasu matan haihuwa; har sai ta kai ga an cire shi ko an yi amfani da magunguna da zai narkar da shi.
Nau’ikan Kari guda uku ne:
- Sin Ta Kulla Yarjejeniyar Tsarin Kafa Huldar Abota Ta Raya Tattalin Arziki Cikin Hadin Gwiwa Tsakaninta Da Kasashen Afirka 22.
- GORON JUMA’A
– Subserosal fibroids
– Intramural fibroids
– Submucosal fibroids
Subserosal fibroids: Wadannan su ne mafi yawan nau’in kari (fibroids.) Sannan suna iya girma, a wasu lokutan kuma suna da tsummoki; wanda ke manne da mahaifa.
Intramural fibroids: Wadannan karin suna tasowa ne a bangon tsoka na mahaifa.
Submucosal fibroids: Wadannan kuma ba su da yawa kamar sauran nau’in karin da ake da su. Domin kuwa za su iya girma a cikin mahaifa kuma suna kuma iya hada wa da tsummoki.
Haka zalika, yana iya haifar da zubar da jinin haila mai yawa tare da haifar da matsalar daukar ciki.
Har kawo yanzu, ba a san sanadin samun wannan cuta ba; amma abubuwa da dama da suka hada da tarihin iyali, kiba, juna biyu da sauransu na iya haifar da wannan cuta.
Kazalika, nau’in wannan kari ga macen da ke tasowa ya danganta da wurin da yake a cikinta ko kuma cikin mahaifarta.
Hadarinsa:
Da zarar mace na tasowa, karin (fibroid) na karuwa; sannan idan tana dauke da guda daya ko fiye da haka a tare da ita, hadarin kara karuwa yake yi, musamman idan ya hadu da daya daga cikin wadannan abubuwa:
1- Kiba
2- Juna biyu
3- Tarihin iyali a kan karin
4- Farkon farawar balaga
Wasu lokutan, kari na iya zama babba tare da haifar da matsanancin ciwon ciki, yana kuma iya haifar da matsala a cikin ciki. A wasu lokutan kuma, ba a ganin wasu alamu kwata-kwata.
Alamomin Kari Sun Hada Da:
-Yawan yin fitsari akai-akai
-Samun karin ciwo a yayin haila
-Jin zafi yayin mu’amalar aure
-Jin zafi a cikin kashin kugu ko baya
-Kumburin ciki
-Wahalar samun ciki
-Dadewar haila fiye da yadda aka saba
Duk wadda ta samu kanta a irin wannan hali, wajibi ne ta gaggauta zuwa asibiti, don ganin likita.
Maganin Kari (Fibroid):
Ana iya magance wannan kari (fibroid), ta hanyar amfani da magunguna ko kuma ta hanyar yin aiki (tiyata).
Daga taskar Dakta Nura Salihu Adam (Salihannur).