Assalamu alaikum masu karatu, barkan mu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirinmu mai farin jini da albarka na Ado Da Kwalliya.
A yau shafin namu zaiyi bayani ne dangane da zubewar gashi:
- Shugaba Xi Ya Ba Da Umarnin Karrama Wasu Mutane 15
- Me Ya Haddasa Cacar Baki Tsakanin Kwankwaso Da PDP?
Tsarabar ta yau bayani ne dangane da zubewar gashi wato ‘Hair Loss’ a turance, ko kuma Alopecia a yaren likita na nufin wani yanayi da mutum kan tsinci kansa na zubewa ko raguwar adadin gashin kansa akalla kwaya 100 a kullum a hankali-a hankali tare da kakkaryewarsa, ko ganin ya taho ya makale jikin abin taje kai, ko kuma ma mutum ya samu kansa gaba daya babu gashin ko gashin ya zube ya maida shi mai sanko haka, bayan zuwa da wani zazzabi, ciwon kai ko kuraje.
Yanayi ne da kan faru ga maza da mata, manya da yara. ma’ana dai ba wanda matsalar ta bari in ana maganar jinsi sai dai duk da hakan ba kowa ke haduwa da matsalar ba, sannan akwai wasu abubuwa na daban dake kara kusanta wasu da larurar.
Ire-iren zubewar gashi:
1. Akwai zubewar gashi baki daya na kai wato (alopecia totalis) 2. Akwai zubewar gashin iya kai wanda yake tsalmi-tsalmi kamar makero. 3. Akwai zubewar gashin kai hade da na jiki baki daya wato ko ina mutum ya rika ganin ba gashi jikinsa musamman gashin gira, gemu a maza, ko gashin ido (Alopecia unibersalist) a turance
Me yake jawo hakan:
Takamaimai ba asan meke jawo hakan ba, amma dai akwai wasu abubuwa daban-daban wadanda suka hada da:
1. Kwayoyin halitta na gado, wato wasu suna gadar hakan ne daga iyaye ko kakanni sakamakon wani sindarin halitta da su magabatan suka rasa, irin wannan zubewar gashin muna kiransa da (alopecia areata) a turance
2. Akwai zubewar gashi sakamakon kwayoyin garkuwar jikin mutum dake bashi kariya ta hanyar yaki da kwayoyin cuta a jika wanda a warshe suke komawa su rika cin sinadaran dake samar da gashin bisa kuskuren cewa kwayoyin cuta ne suka shigo jiki alhalin ba haka abin yake ba, wato (Auto immune)
3. Sai zubewar gashi sanadiyyar karancin sinadarin rayuwa dake taimakawa fitowar gashi da ake kira (androgen) a turance.
4. Zubewar gashi sakamakon haduwa da wata larura dake bukatar shan magani a kai- a kai musamman masu ciwon suga, ciwon makoko (thyroid problems), maganin ciwon sanyin kashi wato ciwon gwiwoyi hannu da kafa, maganin hawan jini, da ciwon Kansa, abu ne da ba komai ba a tsakaninsu.
4. Sai zubewar gashi ko sanko musamman ga maza sakamakon yawaitar sinadarin testestorone a jiki.
5. Idan mutum na karbar radiation therapy a kansa, wato amfani da zafi yayin kone wasu kwayoyin cuta a jiki akan mutum musammn cutar kansa. 6. Sai canjin sinadaran halitta wanda hakan kan faru ne kurum, yayin da mace ta sami juna biyu ta cimma shekarun daina haila ko bayan an haihu.
7. Sai fama da stress wato matsananciyar damuwa afili ko kuma a cikin ciki wato physical or emotional stress a turance. 8. Yawan canza salon kitse-kitse da gyare-gyaren gashi, wadannan su ne mahimman abubuwan da suke jawo zubewar gashi.
Waye yake cikin hatsarin kamuwa da hakan?
1. Mahimmin abin da ke jawo mutum ya fuskanci zubewar gashi shi ne gado (Genetic predispositions) idan har a cikin dangi ko aka sami mahaifiya kanta ta taba ko ta yi fama da shi, to kema a matsayin ‘ya za ki iya gada. Idan aka ce gado ba sai iyaye wanda ka sani ba hatta kakarki ta 10 da ko a tarihi mamarki ko babanki ma basu san zancenta ba kina iya daukowa daga ita ta hanyar iyayenki walau dangin uwa ko na uba.
Kuma wannan shike dauke da kaso 85 cikin dari.
Sauran kaso 15 din duk kurum sun taru ne a:
2. Shekaru wato shekarun tsufa, a lokacin tsufa abu ne da yake ba larura ba don an ga gashi na zubewa, haka kuma musamman macen da ta fara manyanta ta cimma shekarun daina haila shekara 40 zuwa 50 a duniya.