Jama’a barkanmu da Juma’a, barkanku da kasancewa tare da wannan shafi na Goron Juma’a. Shafin da ke ba wa kowa damar mika sakon gaishe-gashensa zuwa ga ‘yan uwa da abokan arziki na kusa, da na nesa.
A yau ma ina dauke da wasu sakonnin gashe-gashen, sai dai kuma kafin na je ga sakonnin masu karatu da suka aiko, sai na fara da mika tawa gaisuwar zuwa ga dukkannin ma’aikatan wannan gidan jarida mai albarka ta LEADERSHIP HAUSA, musamman ma Editana Abdulrazak Yahuza Jere, da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya, kuma da fatan an yi kwalliyar Juma’a tare da kai ziyara lafiya. Sai sakonnin da kuka aiko kamar haka.
Sako daga Usman Sani Amar daga Abuja.
Assalamu alaikum! Barkanmu da Juma’a al’umar Musulmi baki daya da ma’akatan gidan wannan jarida mai albarka. Ina gaida iyayena da ‘yan uwana maza da mata ina musu barka da Juma’a tare da fatan alkhairi Allah ya maimaita mana amin.
Sako daga Abdurrahman Tijjani:
Assalaikum alaikum!
Al’umar Musulmi, ina yi wa kowa fatan alkhairi tare da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya, Allah ya maimaita mana. Ina gaida iyayena ina yi musu fatan alkhairi da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya, Allah ya maimaita mana. Sannan kuma ina gaida ‘yan uwana yayyyena da kannena da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya. Ina gaida yayye iyaye da kannen su tare da yi musu fatan an yi Sallar Juma’a lafiya. Sannan ina gaida ‘yan uwa da abokan arziki da fatan kowa yana cikin koshin lafiya tare da barka da Juma’a.
Sako daga Aisha Rabi’u
Ina mika sakon gaisuwa ta zuwa ga mijina, ina mika sakon gaisuwa ta zuwa ga iyayena da fatan alkhairi ina fatan Allah ya jikan mahaifiyata, ina mika sakon gaisuwa zuwa ga ‘ya’yana da ‘yan uwa da abokan arziki na gida da na waje da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya, ina mika sakon gaisuwa zuwa ga daukacin Musulmi tare da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana amin ya Allah.
Sako daga Khalid Sani
Assalamu alaikum! Ina mika sakon gaisuwa ga ma’aikatan wannan gidan jarida na LEADERSHIP Hausa tare da mika godiya ta da suka bani dama na mika sakon gasuwa na gode.
Ina mika sakon gaisuwa ga iyayena ina fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya, ina mika sakon gaisuwata ga ‘yan ‘uwana ‘ya’yana da kannena da fatan suna cikin koshin lafiya, tare da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana.
Sako daga Maryam Umar
Assalamu alaikum, ina mika sakon gaisuwata ga mijina ina yi mishi fatan alkhairi tare da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya ina mika sakon gaisuwata ga iyayena da ‘yan uwana da abokan arziki da al’umar Musulmi baki daya tare da fatan alkhairi da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana Allah ya kawo mana sauki a rayuwarmu amin.
Sako daga Sadiya Mu’azu
Barkammu da warhaka barkammu da wannan lokaci ina mika sakon gaisuwa ta ga mijina ko nace wanda zan aura da fatan alkhairi da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya. Ina mika sakon gaisuwata ga iyaye da yayyye da kannena ‘yan uwa da abokan arziki tare da fata alkhairi Allah ya maimaita mana.