3. Kasancewa cikin damuwa koda yaushe (stress) a turance
4. Me fama da ciwon Siga
5. Me dauke da ciwon kansa 6. Mutumin da kullum yake kara ramewa haka kurum 7. Karancin ingantaccen abinci a jiki wato mutum mai dauke da ciwon yunwa.
Matakan kariya
Abubuwan da mutum zai taimaki kansa musamman mai larurar ko wanda ma bai da ita kuma ba ya fatan ya kamu da su:
1. Wajibi ne mai wannan matsalar ya kauracewa shan taba ko inda ake shanta 2. Dena yin kitse-kitse masu matukar dame kai 3. Tsayar da shan magungunan dake haddasa zubewar gashin, wato in aka ga sakamakon shan maganin wani ciwon gashi na zuba sai asanar wa da likita a canza da wani.
4. A kaucewa bude kai a cikin rana wato ya zamto zafin ko hasken rana na dukan kai. 5. Idan kana da ciwon da baya jin magani wato kansa kuma ana maka chemotherapy, to ka roki likita a samar maka da ‘Cooling Cap’ ta sawa aka hakan na taimakawa
Ta ya likita zai banbance irin zubewar gashin dake damun mutum?
Eh kamar yadda na fada a baya zubewar gashi iri iri ne, shi ya sa magani da ka bai zama dole ya yi ba ko a asibiti sai likita yai binkice a wani lokacin ma an bukaci karin gwaje-gwaje kafin a gane takamaiman irin matsalar mutum.
Wannan zai sa mutum ya yi ta yawan zuwa kananun asibitoci da wuya a ga sauki, haka ko maganin Hausa na gida mutum ke yi sai ya yi ya gaji domin ba ainihin tushen inda matsalar take aka magance ba. Amma dai a hakikanin gaskiya likita ba ya sa akai ga gwaje-gwaje a dalilin zubewar gashi domin abu ne da in ka san aikinka daga yanayin bayanin yadda mutum yake ji za ka fahimci inda abin yake.
Amma In Ta Kama Dole A Asibiti Ana Yi ?.
1- BLOOD TEST: Gwajin jini domin kawar da tunanin wasu sauran cuttukan ko fahimtar inda ciwon yake walau kwayoyin garkuwa ne ke cin jiki a karan kansu, ko kuwa kwayoyin halittun gado ne.
2- SCALP BIOPSY: A kokon kan mu kan sa abu mu dan kankaro sannan mu mika dakin gwaje gwaje aduba wannan abun da muka kankara domin gano ko kwayar cuta ce ta sa hakan ko a’a.
3- POLL TEST: Likita kan duba layukan gashin a hankali tare da gwado jawo shi ko rike tsakiyar gashi da gashi ya fusga don gwada kwarin gashin.
Wanne irin likita ya dace na gani in na je asibiti ?
Wannan matsalace dake cikin dangin larurorin fata, don haka likitan fata shi ake gani wanda muke kiransu da DERMATOLOGIST da yaren likitanci, idan ta kama sai sun nemi dauki to su kan hada karfi da karfe da masana sinadaran jiki wato (ENDOCRINOLOGISTS)