Domin sanya hannun jari mai yawa a fannin hakar ma’adanai da hydrocarbons a duk fadin nahiyar, wanda hakan ya ba shi ikon hakar ma’adanai na Afirka da manyan ma’adinan hydrocarbons, tare da bijirewa duk wani rashin daidaito kan gina wata kafar intanet da kimarta ta kai kiyasin Dala biliyan 7, Benedict Peters, Shugaba kuma wanda ya kafa manhajar Aiteo / Bravura shi ne Gwarzon dan Kasuwa na shekarar 2024.
Benedict Peters na daya daga cikin fitattun ‘yan Nijeriya masu zaman kansu. Babban dan kasuwa sananne, kuma haziki mai aiki tukuru cikin dabaru, a iya cewa yana daga cikin fitattun da sunayensu ya yi fice a kasuwanci a Nijeriya da a Afirka.
- Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Sake Mayar Da Martani Kan Karin Harajin Da Amurka Ta Kakabawa Kasar
- Kasuwannin Kayayyakin Da Ake Yawan Sayen Su A Lokacin Bikin Bazara Goma Sun Inganta Kashe Kudi Sama Da Yuan Biliyan 1.6
Peters ya yi fice a matsayin hamshakin dan kasuwar da karansa ya kai tsaiko a fannoni daban-daban da suka hada da kamfanonin mai da hakar ma’adanai a kasashen Nijeriya, Ghana, Zimbabwe, Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo, Zambia, Tanzania, Mozambikue, Cote d’Ivoire, Saliyo, Guinea Bissau, Namibia, Libya, Afirka ta Kudu, da kuma Switzerland.
Peters ya kasance daya daga cikin manyan ‘yan asalin yankin da ke da arzikin mai da iskar gas. Kuma ya shiga sana’ar ne a farkon shekarun 1990 sannan ya koma kamfanin Mai da Gas wato ‘Ocean and Oil Limited’ (wanda a yanzu ya koma Oando), sannan ya koma kamfani MRS Oil Nigeria Plc, inda ya zama manajan darakta.
Hamshakin dan kasuwar, Peters ya kafa ‘Sigmund Cummunecci’ a 1999, wanda daga baya ya rikide zuwa Aiteo, mai samar da albarkatun mai da iskar gas a duniya, kuma a karshe ya gina Aiteo a matsayin babban mai samar da mai na asali na Afirka.
Peters ya tsunduma cikin harkar mai da iskar gas a matsayin dan kasuwa a shekarar 1999 kuma ya fara gudanar da kasuwancinsa a fannin da ke samar da mai na karkashin ruwa, wato ‘Downstream Sector’. Duk da haka, Aiteo ya zama kamfani mafi girma da ke hako mai a Nijeriya cikin kankanin lokaci.
A cikin 2015, Peters ya havaka darajar Aiteo tare da sayen (OML 29) Babban shingen bakin teku na Afirka Kudu da hamadar Sahara na Dala biliyan 3. A cikin shekara guda na sayen, Aiteo ya inganta yawan samar da mai daga ganga 17,000 na mai a kowace rana zuwa kusan bpd 70,000.
A matsayinsa babban mai samar da makamashi na ‘yan asalin kasar, Aiteo yana havakawa gami da samarwa da kusan ganga 100,000, ya ninka bisa ga kimar farkon kadararsa zuwa Dala biliyan 6 a cikin shekaru uku. Kamfanin yana shirin saka wata Dala biliyan 4.3 don samun karin kadarori a cikin teku, tare da hasashen jimillar 250,000 na bpd a cikin dan gajeren lokaci zuwa matsakaicin lokaci.
Kamfanin Aiteo ya sanya hannun jari a fannin hakar ma’adanai, noma, samar da ababen more rayuwa, samar da wutar lantarki da rarrabawa, tare da samar da hanyar raba kayayyaki cikin sauri da kuma mai da hankali kan biyan bukatun al’ummomin nahiyar ta hanyar yin amfani da wani tsari na musamman na tushen kadara mai mahimmanci, fasaha, kirkire-kirkire, da kuma wasu daga cikin mafi kyawun fasaha da tunanin kasuwanci a fadin masana’antun da ke aiki a ciki.
Kamfanin na kara fadada ayyukansa zuwa kasashe daban-daban a fadin Afirka da ma wasu kasashen waje. Ya kasance ayyuka na kasa da kasa a cikin kasashen DRC, Ghana, Guinea, Laberiya, Zambia, da Zimbabwe.
Aiteo ya samu ci gaba daga mai hako mai a fannin hakar mai na karkashin teku ‘Downstream’ zuwa babban kamfanin makamashi tare da sanya hannun jari a cikin binciken samar da mai a teku. Yana alfahari da cikakkiyar damar samun makamashi da ayyuka, daga zurfin bincike na ruwa ta hanyar samar da wutar lantarki zuwa dillancin isar da ingantattun kayayyakin man fetur.
Kamfanin ya dauki nauyin adana kayayyakin man fetur, ayyuka mai na yau da kullum, samar da wutar lantarki da rabawa, ajiyar dinbin LPG, da tallace-tallace da rarraba kayan albarkatun mai, ciki har da hanyar sadarwar rarraba tallace-tallace.
Rukunin Kamfanin Aiteo Group yana da wani reshe na samar da wutar lantarki – mai suna Aiteo Power Generation Company Ltd, wanda ya lashe kyautar Kamfanin wutar lantarki na Alaoji. Wannan ya ba da damar ci gaba da hada ayyuka don gina cibiyar samar da wutar lantarki a yankin Neja Delta. Ayyukan samar da wutar lantarki an tsara su ne don ciyar da su daga albarkatun iskar gas daga rijiyoyin mai.
Peters yana samar da wani babban tsari na amfani da iskar gas, man fetur, da kwal wajen samar da wutar lantarki da kuma tallata su ga Nijeriya da sauran kasashen yammacin Afirka. Ya yi fatan ayyukan za su taimaka wajen samar da wutar lantarki ga mutane kimanin miliyan 7.6. Babban shirinsa na warware makamashin ya mayar da hankali kan Afirka kuma yana fatan samar da damar yin amfani da hanyoyin samar da wutar lantarki a nahiyar.
Manufarsa ita ce ya ga cewa an samar da isasshiyar iskar gas a Afirka don samar da makamashin lantarki cikin sauki ga al’ummar Afirka a duk inda suke a nahiyar.
Yin amfani da iskar iskar gas shi ne babban ginshiki na kundin makamashi na Peters yayin da ya shiga mataki na gaba na ayyukan bincike da havakawa.
Kamfaninsa yana havaka duk wani nau’i na darajar iskar gas mai tsaka-tsaki na hakar mai a karkashin teku a cikin kawance tare da masu samar da iskar gas a duniya.
Wannan ci gaban ya hada da sanya hannun jari mai yawa a wuraren tattara iskar gas, samar da LPG, ajiya da rarrabawa. Haka nan, ya hada da havaka hanyoyin sadarwa na bututun mai, sarrafa NGL, sufuri da dabaru
Kamfanin Peters’ Aiteo ya sake samun wani gagarumin ci gaba ta hanyar hadin gwiwa da NNPC wajen kaddamar da wani sabon matakin samar da danyen mai mai suna Nemb; ta hanyar wannan hadin gwiwa, kamfanin da aka amince da shi a matsayin babban mai samar da man fetur a nahiyar Afirka, ya kara yawan man da yake hakowa.
Wani kamfani na hadin gwiwa tsakanin kamfanin NNPC na gwamnati da kamfanin mai na Aiteo Eastern E&P Co. Ltd za su gudanar da tallata kamfanin Nembe, kan aikin sayar da danyen mai na farko da wasu sassan Nijeriya ke gudanarwa.
Aiteo, babban mai samar da mai a Afirka, ya taka rawar gani a masana’antar mai ta nahiyar, yana samar da kusan ganga 100,000 a kowace rana kuma yana ba da gudummawar sama da kashi biyar cikin 100 na man da Nijeriya ke hakowa a kullum.
Peters ya sami babban hannun jari a tashar iskar gas ta Mazenga ta Mozambikue, mafi girman ajiyar iskar gas a yankin kudu da hamadar Sahara. An kammala cinikin ne bayan jerin yarjejeniyoyin noma da kamfanin mai na Mozambikue Empresa Nacional de Hydrocarbon (ENH), inda ya sanya Aiteo a matsayin mai kula.
Kaddarorin Mazenga, suna nan a matsugunan ruwa na Mozambikue, sun kai kusan murabba’in kilomita 23,000. An kiyasta cewa suna kunshe da babban tanadi na iskar gas da ya kaia ‘cubic’ triliyan 19.
Aiteo ya kaddamar da babban shirin ci gaba cikin gaggawa, da ya hada da nazarin yanayin sararin samaniya da nazarin karkashin kasa, cikakken binciken fili, da sake fassara da sarrafa bayanan da ke akwai.
A karshe, Peters ya havaka kasuwancinsa kuma ya shiga harkar harkar ma’adanai ta hanyar amfani da Bravura Holdings. Tare da Bravura din ne ya abin kwatance mai karfi a duk fadin Afirka da ba a tava samu ba, yana saka hannun jari a cikin uranium, platinum, lithium, azurfa, jan karfe, da zinare.
Tare da rangwamen ma’adinan da suka bazu cikin kasashen Afirka, ya jagoranci tawagar hako ma’adanai na Dala biliyan daya wanda ke nuna jajircewarsa ga ci gaban tattalin arzikin Afirka.
Bravura Holdings yana aiki a matsayin kamfani mai hadaka a tare da kakkarfan fayil din da ya kunshi zinari, jan karfe, lithium, da kadarorin karfe a Ghana, Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Zambia, Nijeriya, Namibiya, da Afirka ta Kudu. Hannun jarin da ya zuba a Zimbabwe na nuna sadaukarwar Bravura don canza yanayin hakar ma’adanai na Afirka.
Bisa la’akari da irin bajintar da ya yi a fannin mai da iskar gas, Peters ya samu kyautuka daban-daban, ciki har da nada shi ‘Shugaban Man Fetur da Gas na Afirka’ da kyauta Forbes’ Best of Africa Gala a ranar 27 ga Satumba 2018, Markuee Award for Global Business Edcellence.
A bikin bayar da lambar yabon ya jagoranci na Afirka da Amurka a 2014, ya zama gwarzon LEADERSHIP na shekarar 2014 a matsayin Shugaba, da Dr. Martin Luther King Jr. Legacy Awards a fannin karfafa tattalin arziki a shekarar 2015.
An ambace shi cikin ‘Yan Nijeriya 50 da suka fi Tasiri a shekarar 2017 ta BusinessDay kuma Guardian ta amince da shi a matsayin ‘Man of the Year’ a shekarar 2018.