Kawo yanzu za’a iya cewa dan wasa Karim Benzema ya lashe gasar La Liga da kofin zakaru na ‘Champions League’ a kakar wasa ta 2021 zuwa 2022, ya kuma ci kwallo 44 a wasanni 46 wanda hakan ya sa ake ganin ko zai iya daukar kyautar Ballon d’Or a bana kuwa? Mai shekara 34, zai zama mai yawan shekarun haihuwa idan ya lashe kyautar bana, bayan dan kwallon Blackpool, Stanley Matthews, wanda ya zama zakara a shekarar 1956 kamar yadda tarihi ya nuna.
Mai tsaron ragar Real Madrid, Thibaut Courtois shi ne ya lashe kyautar dan wasan da ya fi taka rawar gani a ranar Asabar a Faransa, sannan shima dan wasa Binicius Jr ne ya ci kwallon da Real Madrid ta doke Liberpool 1-0 da ta dauki kofi na 14 jumulla sai dai Benzema ya taka rawar gani a karawar, har da cin kwallo amma ba a karba ba.
Wasu na ganin dan wasan tawagar Faransa, ya cancanci ya lashe Ballon d’Or ta kakar nan da za’ayi bikin bayar da kyautar ranar 17 ga watan Oktoba saboda ana ganin ba kamarsa a turai a kakar bana. Bayan da Real Madrid ta lashe La Liga da Champions League, Benzema ne kan gaba a cin kwallaye a babbar gasar kwallon kafa ta Sifaniya da kuma ta Zakarun Turai ta kakar nan da aka kammala.
Kawo yanzu ya zura kwallo 27 a La ligar nan da tazarar tara tsakaninsa da na biyu, sannan ya ci 15 a Champions League, kenan duk minti 74 ya ci, sannan Benzema ya zura kwallo 10 a raga daga zagaye na biyu a 15 din da ya ci a Champions League a bana.
Dan wasan ya kuma zura kwallaye uku rigis a raga a karawa da kungiyoyin Paris St-Germain da Chelsea, kuma shi ne ya ci kungiyar Manchester City kwallo ta karshen da ta kai Real Madrid wasan karshe.