Babbar kotun tarayya da ke zamanta a jihar Kano, ta ayyana ranar 22 ga watan Satumbar 2023 domin yanke hukunci kan karar da tsohon gwaman jihar Kano Abdullahi Ganduje ya shigar a gabanta, inda ya bukaci kotun da ta dakatar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar daga bincikensa.
A yau Talata ne, Babban Lauyan da hukumar ta dauko, SAN Femi Falana, ya tsaya kai-da-kafa cewa, kariyar da tsohon Gwaman ke da ita ta kare tun a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Don haka, babu wata kotu a kasar nan, da ke da ikon bawa Ganguje ko iyalansa ko kuma kwamishinoninsa wata kariya.
Sai dai, Lauya mai kare Ganduje a gaban kotun ya bayyana cewa, ba a bi ka’idar kare ‘yancin dan Adam ba.