Hukumar tace Fina-finai ta Jihar Kano ta ɗauki tsauraran matakai kan wasu jaruman Kannywood guda uku da suka hada da Usman Soja-boy, Shamsiyya Muhammad, da Hasina Suzan, bisa abinda suka kira rashin da’a da jaruman suka yi a wani faifan bidiyo na waka.
Hukumar ta haramta wa waɗannan jaruman shiga duk wani fim ko bidiyo da za a shirya a jihar, a cewar hukumar, “ba za a amince da ɗabi’un da jaruman suka nuna a faifan bidiyon ba, saboda hakan, ya saba wa kyawawan ɗabi’un jihar”.
Hukumar ta kuma bayyana cewa ba za ta amince da duk wani fim ko bidiyo da ke ɗauke da wadannan ‘yan wasan da aka dakatar ba.
Bugu da kari, hukumar ta sake nanata haramcin da ta yi a baya kan jaruma Samha M. Inuwa, wadda ita ma aka same ta da laifin rashin ɗa’a, wannan mataki da hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta ɗauka na da nufin bunkasa kyawawan ɗabi’u da da’a a harkar nishaɗi.