Shahararren Bikin Rigata da Al’adu na Yauri zai gudana ne daga ranar 8 zuwa 10 ga Fabrairu, 2024 a tsohon birnin Yelwa-Yauri a Jihar Kebbi.
Shugaban bikin na kasa wanda shine sakataren gwamnatin jiha Alhaji Yakubu Bala Tafidan Yauri ne ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai a Birnin Kebbi.
- Gwamna Nasir Ya Amince Da Fitar Da Naira Miliyan 27.5 Don Biyan Kuɗin Ɗaliban Lauyoyi Na Jihar Kebbi
- Auren Gata : Gwamnatin Jihar Kebbi Ta Aurar Da Mata 300
Taron zai gabatar da kaddamar da littafi kan tarihin Yauri daga 1411 zuwa yau, baje kolin kasuwanci, baje kolin amfamin gona, wasan kwaikwayo na al’adu da babban wasan karshe na Rigata.
Mai martaba Sarkin Yauri na 42, Dr. Muhammad Zayyanu Abdullahi ne ya dauki nauyin sake farfado da bikin na Rigata da gwamnatin jihar Kebbi ta dauki nauyinta a matsayin babban taron al’adun.
Rigata kalma ce a yaren yankin Gungawa da ke nuna yakin ruwa.
Bikin ya kunshi motsa jikin koguna da suka hada da wasannin ruwa da kuma nishadantarwa wanda aka fara shekaru 200 da suka gabata a matsayin nunin karfin sojojin ruwa na ‘yan bindigar Gungu inda mayakan na Gungu suka kai hari a kan kogin Niger mai hatsarin gaske.
Sai dai mayaƙan sun kasance suna hawa kwale-kwale masu girma dabam da makamai daban-daban domin kai farmaki kan mamayabin da ke cikin ruwa.
Har ila yau, motsin ruwa ya kasance a matsayin atisayen horar da mayaka na Gungu masu zuwa.
Zuwan Turawa ya sa gwamnatin mulkin mallaka ta hana farautar kadodin ruwa don kiyaye irin wannan nau’in.
Bayan haka, Rigata ta zama babban baje kolin arziki, iko da tasiri yayin bukukuwan aure na manyan gidaje.
Lamarin ya ci gaba har zuwa ziyarar da Marigayi Firimiyan Arewacin Nijeriya Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto ya kai Yelwa-Yauri inda aka shirya Rigata tare da nuna amfani gona domin karrama Firimiya.