Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina ya yi fatali da kyautar raguna 100 da wani mai kudi a jihar ya yi masa.
Jaridar The Guardian ta tattaro cewa, an kai ma Gwamna Radda ragunan ne a jiya Talata, gabanin bikin Sallah na yau, amma ya yi fatali da tayin kyautar.
Ma’aikatan gidan gwamnatin sun ce, tayin kyautar ya bata wa gwamnan rai, inda ya yi gargadin cewa, kar wani ya kara kawo masa irin wadannan kyaututtuka a nan gaba.
Gwamnan ya yi mamakin yadda wasu masu kudi za su dinga bayar da kyaututtuka ga masu rike da mukaman jagoranci bayan ga masu kananan karfi nan da yawa a tare da su wadanda suka fi cancanta da a taimakawa.
Don haka, Radda ya yi kira ga masu hannu da shuni da su yi amfani da lokacin bukukuwa don taimakawa talakawa.
Gwamnan ya yi kira ga Kiristoci da Musulmai da su yi amfani da bukukuwan Sallah domin samar da zaman lafiya a tsakaninsu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp