Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin Tinubu za ta ba da himma cikin gaggawa wajen magance tabarbarewar ababen more rayuwa a kasar nan.
Shettima ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Laraba a lokacin da ya kai gaisuwar Sallah ga Shehun Borno, HRH, Abubakar Ibn Garbai El-Kanemi a Maiduguri.
A cewar wata sanarwa da ofishin yada labaransa ya fitar, Shettima ya ce za a magance dukkan kalubalen samar da ababen more rayuwa a kasar da suka hada da hanyar Gamboru Ngala, Dikwa da kuma hanyoyin Damboa a jihar Borno.
A nasa jawabin, gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Zulum, ya yaba da kyawawan halayen mataimakin shugaban kasa a matsayinsa na mutum mai kishin al’umma, dan siyasa mai kishin kasa, inda ya kara da cewa kasancewa, wannan ce ziyarar farko da mataimakin shugaban kasa Shettima ya kai jihar tun bayan komawarsa Abuja, amma ziyarar ta bada fa’ida mai muhimmanci sosai ga mutanen Borno.”
Shi ma a nasa jawabin maraba, Shehun Borno, Abubakar Ibn Garbai El-Kanemi, wanda ya yi jawabi a yaren Kanuri, ya yaba wa mataimakin shugaban kasa a matsayinsa na cikakken dan jihar Borno.