Bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin na duniya (CIIE) ya nuna kudurin kasar Sin na hada kan duniya domin cin gajiyar juna ta fuskar tattalin arziki har ma da zamantakewa.
A karon farko da na samu labarin bikin, na yi tunanin akwai yiwuwar za a bar ’yan kasuwarmu na Afirka da dama a baya wurin shiga a dama da su, saboda rashin karfin jari irin na takwarorinsu na sauran duniya.
- Xi Zai Gana Da Biden Tare Da Halartar Taron Shugabannin Tattalin Arzikin APEC
- Sin Na Taka Rawar Gani Wajen Tabbatar Da Zaman Lafiya A Gabas Ta Tsakiya
Amma bisa bayanan da na ji daga cibiyar baje kolin, a ziyararmu ta aiki a 2018 a Shanghai, shugabannin shiryawa sun ce, baje kolin na CIIE ya tsara taimakawa kasashe masu rauni wajen ba su matsugunai domin baje kolinsu ba tare da biyan kudi ba har ma da wani tallafi da zai taimaka wa kayayyakinsu su samu damar shiga kasuwar kasar Sin.
Wannan tsari ya haifar da da mai ido, domin ko a bana, daga kasar Zimbabwe kawai, fiye da kamfanoni da kungiyoyi 15 da suka kware a fannin fasahar zane, da sarrafa kayayyakin fata, da harkokin sadarwa, da kuma sayar da ma’adanai, suke halartar bikin baje kolin.
Haka nan daga Nijeriya da Afirka ta Kudu da sauran kasashe duk suna can ana damawa da su a bikin baje kolin na bana karo na 6 a birnin Shanghai.
Baje kolin na CIIE, karin dama ce ga Nijeriya ta samun cinikin kayan da take fitarwa zuwa Sin kamar su kwarar manja, ridi, ‘ya’yan itace, hatsi har ma da waken soya wanda cinikayyarsu sun kai Dalar Amurka miliyan 140.88 a shekarar 2021, bisa bayanan cibiyar cinikayya ta COMTRADE ta Majalisar Dinkin Duniya.
Shugaban Tsangayar Aikin Gona da Raya Karkara ta ARMTI da ke Nijeriya, Dr. Olufemi Oladunni, ya bayyana cewa, “akwai damammaki da yawa da manoman Nijeriya za su ci gajiya a kasuwanni na kasashen duniya bisa cudanya da ‘yan kasuwa na waje, manoman za su samu dabarun inganta noma, da yadda za su rika sarrafa amfanin gona bayan girbi da kuma fitarwa waje.”
Har ila yau, manajan daraktar kamfanin sarrafa kayan fata na Samuneti dake Zimbabwe, Tsitsi Chirova, ta ce baje kolin CIIE fage ne da suke samun damar fadada hadin gwiwa da kara fahimtar ire-iren kayayyakin da za su rika sarrafawa. “Daga shigar da muka yi a baya, mun sami damar habaka tallace-tallacenmu, da kuma samun shawarwari daga abokan cinikinmu don habaka abubuwan da muke samarwa. Don haka idan muka halarci bikin baje kolin na kasar Sin, na yi imani hakan zai tallata kamfaninmu da gaske, kuma bayan mun dawo gida, mun yi imanin za mu samu karin kwastomomi,” in ji ta.
Shi ma wani mai sassaka dake birnin Harare, Richard Mudinzva, da ya sha alwashin halartar bikin karo na 6, ya ce, akwai abokan ciniki da yawa a kasuwar kasar Sin dake sha’awar kayayyakin Afirka. Alkaluman da ofishin jakadancin kasar Sin dake Zimbabwe ya fitar sun nuna cewa, cinikayyar bangarorin biyu ta karu da kashi 39.4 bisa dari, zuwa dala biliyan 2.43 daga Janairu zuwa Satumbar 2023, wanda ya zarce adadin cinikin da aka samu a shekarar 2022.
Kasar Guinea-Bissau, mafi noman kashu a duniya, ta ci gajiyar bikin baje kolin a bara, yayin da aka ware mata matsugunin kamfanoninta suka baje kolinsu na kashu. Kamar yadda jakadan kasar a Sin, Antonio Serifo Embalo ya bayyana, sakamakon halartar bikin baje kolin na bara, ’yan kasuwa da dama sun nuna muradinsu a kan bangaren kashu na kasar. Wasu ma tuni har sun tsara yadda za su zuba jari a kasar.
A nashi bangaren, mataimakin shugaban Afirka ta Kudu, Paul Mashatile, ya yaba wa kasar Sin bisa yadda take kara bude kofofinta na kasuwanci musamman ga kasashen Afirka. Yana mai cewar, bikin baje kolin ya kara fadada dama ga kamfanoni na duniya wajen bunkasa hulda da abokan ciniki.
Sama da kamfanoni 1,500 daga kasashen dake cikin shawarar “ziri daya da hanya daya” ke baje kolin hajojinsu a bikin karo na shida.
Ana sa rai, cinikayyar shigo da kaya na kasar Sin su zarce dala tiriliyan 17 nan da shekara 5 masu zuwa, don haka nake cewa, kasashen Afirka kar ku yarda a bar ku a baya wajen cin gajiyar hakan.