Sakamakon kudirin da kasar Sin da Afirka suke da shi na yin aiki tare domin cin gajiyar juna da kuma hobbasar da Sin ke yi na tabbatar da al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya a duniya, a wannan makon ne aka bude bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka karo na uku, daga ranar 29 ga watan Yuni zuwa ranar 2 ga watan Yuli a birnin Changsha na lardin Hunan da ke tsakiyar kasar Sin.
Baje kolin wanda aka fara a shekarar 2019, ya kasance wani muhimmin dandali na inganta hadin gwiwar kasuwanci da tattalin arziki tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Shekaru 14 ke nan a jere, kasar Sin tana zama babbar abokiyar kasuwanci a Afirka, bayan da ta doke Amurka a wannan fannin a shekarar 2009. Kawancen cinikayya da tattalin arzikin ba wai kawai ya zurfafa ba ne, har ma ya kara samun tagomashi tare da cin gajiyar abin a tsakanin Sin da Afirka.
Adadin cinikayya a tsakanin Sin da Afirka ya kai Dala biliyan 282 a shekarar 2022, inda ya ninka wanda yake tsakanin Amurka da Afirka a shekarar har sau hudu. A cikin shekaru 10 da suka wuce, kasar Sin ta kasance kan gaba a matsayin kasar da ta fi zuba jari a Nahiyar Afirka, inda ta kara habaka tattalin arzikin nahiyar da kashi 20 cikin dari. A cikin rubu’in farko na shekarar 2023, sabon jarin da kasar Sin ta zuba kai-tsaye a Afirka ya bunkasa da kashi 24 bisa dari a shekarar da ta gabata, inda ya kai na Dala biliyan 1.38.
Hadin gwiwar kasuwanci da tattalin arziki yana daya daga cikin hanyoyi mafi dacewa na kawar da talauci da rashin ci gaba. Dangane da hakan, tun bayan kafuwar dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka (FOCAC) a shekarar 2000, shugabannin Sin da Afirka, suke ba da fifiko wajen daidaita tattalin arzikin duniya a matsayin wata manuniya ko babbar alama ta hadin gwiwarsu. Haka nan an shigar da tsarin cikin shirye-shirye da manufofi daban-daban ciki har da na Ziri Daya Da Hanya Daya (BRI).
Manufar bude kofar kasuwanci ta kasar Sin ta shawo kan yadda kayayyakin Afirka ke tabarbarewa a kasuwannin kasar. Kasar Kenya ta zama kasa ta farko a nahiyar Afirka da ta fitar da danyen kayan marmari na avocado zuwa kasuwannin kasar Sin. A cikin watanni uku, tsakanin Maris da Mayun 2023, ta fitar da kayan marmarin zuwa kasar Sin da ya kai na Dala miliyan 64.38, wanda ya amfanar da dubban kananan manoma. A yau, kasashe 21 na Afirka suna cin moriyar yafe musu biyan haraji na kashi 98 bisa dari na kayayyakin da suke fitarwa zuwa kasuwannin kasar Sin.
Akwai abubuwa masu yawa da ke kara habaka hadin gwiwar kasuwanci tsakanin Sin da Afirka. Alakar da Sin ke yi da kasashen Afirka, na mayar da hankali ne da ba da fifiko kan hadin gwiwar tattalin arziki da gudanar da harkokin kasuwanci. Wannan ya sha bamban sosai da tsarin da Amurka ta dauka na hulda da nahiyar da ke katsalandan gare su da sunan “dimokuradiyya,” “sha’anin mulki,” da “`yancin Dan adam.”
Har ila yau, huldar kasuwanci da ke tsakanin kasar Sin da Afirka ta ginu ne bisa la’akari da abubuwa na bukatu da samar da wadata kawai. Hakazalika, masu zuba jari na kasar Sin suna kallon Afirka a matsayin wurin samun damammaki. A daya bangare kuma, kasashen yammacin duniya da masu zuba jarinsu su kan yi wa Afirka kallon wani yanki na yi wa kawunansu garkuwar tsaro sannan akwai karancin harkokin tattalin arziki. Misali jarin da Washington ta zuba kai tsaye a Afirka ya ragu daga Dala biliyan 69 a shekarar 2014 zuwa Dala biliyan 47.5 a shekarar 2020.
Sakamakon kudurorin taron ministoci karo na 8 na FOCAC a shekarar 2021, Sin da Afirka suna da damar amfani da bikin baje kolin, da zurfafa hadin gwiwa a fannonin da suka fi ba da fifiko kamar kiwon lafiya, rage fatara, aikin gona da samar da abinci, inganta kasuwanci, zuba jari, kirkire-kirkire na zamani da bunkasa kyawon muhalli.
Bikin baje kolin na Changsha na zuwa ne a wani muhimmin lokaci ga Sin da Afirka. Shi ya sa bangarorin biyu ke aiki tukuru domin kawar da tasirin da annobar COVID-19 ta yi. Afirka na aiwatar da kyakkyawan tsarin ciniki cikin ‘yanci na nahiyar (AfCFTA) wanda ya hada hada-hadar kasuwanci na mutane biliyan 1.4 tare da jimillar kudin kayayyakin cikin gida(GDP) da ya haura Dala triliyan 3.7.
A lokaci guda kuma, kasar Sin tana kara sa kaimi wajen bunkasa tattalin arzikin duniya ta hanyar habaka hada-hadar kayayyaki, karfafa jari, fasahohi da ka’idojin gudanarwa mafi dacewa. Matukar babu kakkarfan kawancen kasar Sin, yunkurin Afirka na bunkasa masana’antu zai iya zama a mafarki kawai. Hakazalika, Afirka ba tana bai wa kasar Sin damar kasuwancin kayan masana’antunta ne ba kawai, har ma da sararin zuba jari mai dorewa tare da dimbin albarkatun kasa da ake bukata domin sarrafawa a masana’antu na zamani.