An bude bikin cinikayyar hidimomi ta kasar Sin ko CIFTIS a yau Laraba a birnin Beijing.Bikin zai ci gaba da ci har zuwa 13 ga watan da muke ciki a Shougang Park, inda mahalarta daban-daban daga kasashe 90 da kungiyoyin duniya ke halarta, sannan kamfanoni sama da 1800 ke nuna kayayyakinsu.
Daga ciki akwai guda 473 da ke cikin manyan kamfanoni 500 na mujallar Fortune Global da sauran manyan masana’antu da suka hada da Honeywell, Johnson & Johnson da kuma kamfanin Siemens.Biki na bana an yi masa lakabi da “Samar da hidimomi da bunkasa ci gaba ga kowa’’, inda za a gabatar da taruka da aikace-aikacen bunkasa kasuwanci.
Mataimakin shugaban kasar Zimbabwe, Constantino Chiwenga, ya ce ana kyautata zaton baje kolin zai samar da damammakin zuba jari a tarukan da za a gudanar, da holen kayayyaki, ababen more rayuwa da fasahohin zamani, yana mai karawa da cewa, hakan zai taimakawa kasarsa wajen gano damarmakin kasuwancin kayayyaki, da karfafa shigo da kayayyaki da jawo hankalin abokan hulda a fannonin fasaha, yawon bude ido, ilmi da lafiya.
Bayanan da aka fitar na kwanan nan ya nuna cewa, a watanni bakwai na farkon shekarar nan, cinikayyar hidimomi da kasar Sin ta yi, ya kai adadin kusan Yuan tiriliyan 4.45 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 656.6, wanda ya karu da kaso 8.3 da ake samu a duk shekara. (Mai fassara: Suleiman Suleiman Ibrahim)














