Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa, Shugaban Ƙasa Tinubu na aiwatar da wasu tsare-tsare da sauye-sauye da aka tsara domin magance kura-kuran da aka yi a baya da kuma sanya Nijeriya ta zama wata babbar ƙasa mai ƙarfin tattalin arziƙi nan gaba kaɗan.
Idris ya bayyana haka ne a cikin jawabinsa a Abuja ranar Alhamis a wani taron da aka yi na manema labarai domin bayyana abubuwan da aka shirya domin bikin cikar Nijeriya shekaru 64 da samun ‘yancin kai.
- Manyan Batutuwan Taron Sanatoci Kan Gyaran Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya A Kano
- Tinubu Ya Naɗa Kwamitin Gudanarwa Na Hukumar Cigaban Yankin Arewa Maso Yamma
“A ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Tinubu, mun ɓullo da tsare-tsare da sauye-sauye da nufin gyara kura-kuran da aka yi a baya da kuma mayar da Nijeriya matsayin mai ƙarfin tattalin arziƙi nan gaba kaɗan. Duk da halin da tattalin arziƙin duniya ke ciki da kuma raɗaɗin da ke tare da wasu sauye-sauyen, Shugaban Ƙasa ya ci gaba da mai da hankali kan ƙoƙarinsa na farfaɗo da tattalin arziƙinmu da kuma maido da ƙasar kan turbar wadata da ci gaba mai ɗorewa,” inji shi.”
Ministan ya bayyana cewa, a wani gagarumin yunƙuri na kawo sauyi ga ci gaban zamantakewa da tattalin arziƙin karkara a Nijeriya, Shugaban Ƙasa Tinubu ya yi nasarar nema tare da samun gagarumin hukuncin kotun ƙoli da ya ba wa ƙananan hukumomi cin gashin kai.
Idris ya ce, wannan shawara guda ɗaya ya tabbatar da cewa, zaɓaɓɓun ƙananan hukumomi a yanzu suna da ikon sarrafa kasafin kuɗi kai tsaye, wanda zai inganta tsarin mulki da ci gaban ƙananan hukumomi.
“Bugu da ƙari, ana aiki sosai wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziƙi, daidaita tsarin musayar kuɗaɗen waje, sake fasalin tsarin haraji don inganta shi, da rage nauyi a kan ‘yan Nijeriya, sake daidaita ɓangaren man fetur da iskar gas ɗinmu don jawo sabbin jari, da kuma ba da fifiko wajen rarrabawa da faɗaɗa kuɗaɗen shiga na gwamnati,” inji shi.
Ministan ya ƙara da cewa sannu a hankali Shugaban Ƙasar yana jagorantar Nijeriya ta shiga wani yanayi na canjin makamashi na musamman ta hanyar ƙaddamar da shirin shugaban ƙasa na matsar da ƙasar daga amfani da man fetur zuwa iskar iskar gas (CNG) a matsayin makamashin ababen hawa da injina.
Ya amince da cewa ci gaba da fitar da CNG da kayayyakin da ke da alaƙa da su yana rage tsadar sufuri ga ‘yan Nijeriya da kashi 60 cikin 100, da samar da ayyukan yi, da kuma jawo dubun-dubatar daloli a cikin gida da waje.
“Ta hanyoyi da yawa Shugaban Ƙasa ya mayar da hankali wajen sanya ƙarin kuɗaɗe a aljihun al’ummar Nijeriya, da samar da hanyoyin samun ci gaba mai ɗorewa,” inji shi.
Ministan, wanda ya ce bikin cika shekaru 64 da samun ‘yancin kai lokaci ne na tunani, biki, da sabunta fata, ya jaddada cewa ya zuwa yanzu Nijeriya ta nuna juriya, ƙarfi, iyawa, da kuma jajircewa wajen fuskantar ƙalubale masu tarin yawa.
Idris ya ce tun bayan samun ‘yancin kai a shekarar 1960, Nijeriya ta samu ci gaba daga ƙasa mai fata ta zama ƙasa mai ƙarfin faɗa a ji a nahiyar Afirka kuma mai martaba a duniya kuma duk da ɗimbin ƙalubalen da ake fuskanta, ƙasar na ƙara samun ƙarfi ta hanyar hangen nesa mara kaushi na ƙasa mai haɗin kai da wadata.
Ministan ya yi amfani da wannan dama wajen yaba wa ‘yan Nijeriya kan haƙuri da juriya da suka nuna a wannan lokaci mai matuƙar wahala a cikin sauyin tattalin arziƙin ƙasar, inda ya ce tafiyar ta yi tsauri amma akwai haske a ƙarshe.
Ya ce a kwanan nan ne Majalisar Zartaswa ta Tarayya ta amince da Yarjejeniyar Ɗa’a ta Ƙasa, wanda yanzu Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai za ta fara aiwatarwa daidai da ƙudurin Shugaban Ƙasa na farfaɗo da ɗabi’u, ɗa’a, da kuma al’adu.
“Yarjejeniyar za ta ƙarfafa imanin cewa abubuwan da suka haɗa kawunanmu-kishin ƙasarmu, wajibcinmu ga ƙasarmu, da wajibcinta a gare mu – za su kasance masu ƙarfi da zurfi fiye da abin da ke son raba mu,” inji shi.
Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ne ya ƙaddamar da shirye-shiryen bikin cika shekaru 64 da samun ‘yancin kai, wanda ya samu halartar Ministan Kasafi da Tsare-tsare na Tattalin Arziƙi, Sanata Atiku Bagudu; Ministan Kuɗi da Gudanarwa na Tattalin Arziƙi, Mista Wale Edun; Ministan Ayyuka, Sanata Dave Umahi; Ministan Albarkatun Ruwa, Farfesa Joseph Utsev; Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman; Ministan Yawon Buɗe Ido, Lola Ade-John; Ministan Ayyuka na Musamman da Harkokin Gwamnati, Zaphaniah Jisalo, da sauran manyan jami’an gwamnati da mataimakan Shugaban Ƙasa.