• English
  • Business News
Friday, October 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bikin Kafuwar Daular Saudiyya Shekara 93: Abubuwan Da Suka Kamata A Sani

by Sulaiman
2 years ago
Saudiyya

Ofishin Jakadancin Kasar Saudiyya da ke Abuja ya gudanar da bikin cikar ranar kasa ta Saudiyya karo 93 a gidan Ambasadanta da ke Abuja, wanda ya samu halartar jami’an gwamnati da shugabannin ofisoshin diflomasiyya da kungiyoyin kasa da kasa da kuma ‘yan kasuwa da sauran manyan mutane.

A nasa jawabin, Jakadan kasar Saudiyya a Nijeriya H.E. Faisal bin Ebraheem Alghamdi ya bayyana cewa, Masarautar tana bikin cika shekaru 93 na hadin kan sassan Masarautar Sarki Abdulaziz bin Abdulrahman Al Saud (Allah Ya jikansa) a karkashin wata kungiya mai karfi wacce aka kafa ta bisa akidar Musulunci wacce daidaito, adalci da amana suka tabbata acikinta.

  • Gwamnatin Kaduna Ta Nemi Saudiyya Ta Zuba Jari A Jiharta
  • Saudiyya Ta Kebe Wa Nijeriya Kujeru 95,000 A Aikin Hajji Na 2024

Alghamdi ya kuma bayyana cewa, akwai kyakkyawar alaka a tsakanin Masarautar da Nijeriya mai cike da tarihi wacce ta ke ta ci gaba da bunkasa tun lokacin da aka kulla huldar jakadanci tsakanin kasashen biyu a shekarar 1961. Ya kuma yi fatan alheri da nasara ga mai girma shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Yayin da yake tsokaci kan kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasashen biyu, jakadan ya ce, sama da mahajjata ‘yan Nijeriya 200,000 da masu zuwa karamin aikin hajji (Umara) da maziyarta sun ziyarci Masarautar a shekarar da ta gabata, kuma Masarautar ta baiwa daliban Nijeriya tallafin karatu sama da 200 don yin karatu a jami’o’in kasar daban-daban. Ya kara da cewa, yawan cinikin da ke tsakanin kasashen biyu ya haura dala miliyan 600.

Saudiyya

LABARAI MASU NASABA

Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka: Ta Bar Baya Da Ƙura

Shugaban Ƙasa Zai Sake Nazari Kan Mutanen Da Aka Yi Wa Afuwa

Akan taimakon jin kai ga al’ummar Nijeriya. Jakadan Masarautar ya bayyana cewa, Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud (Allah Ya kare shi) ya ba da umarnin aiwatar da taimakon sa-kai na Nur-Saudi a Nijeriya, wanda aka fara aiwatarwa mataki-mataki; An aiwatar da matakin farko wanda aka nufi yakar makanta da musabbabanta, sannan kuma ta yi wasu ayyukan tiyata musamman a bangaren mafitsara da raba tagwayen da aka haifa a Jone.

Jakadan ya taya iyayen tagwayen murna da aka yi nasarar raba su a watan Mayun da ya gabata, a aikin tiyata mai lamba 56 da masarautar ta yi wajen raba wasu tagwaye daga sassan duniya.

Saudiyya
A karshe, jakadan ya mika godiya ga kasashen duniya da abokan arziki daga ciki har da tarayyar Nijeriya bisa goyon bayan da ta baiwa Saudiyya na karbar bakuncin bikin baje kolin duniya na 2030 a birnin Riyadh, wanda ya zo daidai da ranar da Saudiyya ta ke shirin kaddamar da kudirinta na shekarar 2030.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Shugaban Najeriya Ya Kaddamar Da Aikin Samar Da Ruwa Da Kamfanin Sin Ya Gudanar A Birnin Abuja
Manyan Labarai

Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka: Ta Bar Baya Da Ƙura

October 17, 2025
Tinubu
Manyan Labarai

Shugaban Ƙasa Zai Sake Nazari Kan Mutanen Da Aka Yi Wa Afuwa

October 16, 2025
Sabbin Ministoci
Manyan Labarai

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Amupitan A Matsayin Shugaban INEC

October 16, 2025
Next Post
Bayan Shekaru 9, Har Yanzu Yana Tuna Ni

Bayan Shekaru 9, Har Yanzu Yana Tuna Ni

LABARAI MASU NASABA

Ƙungiyar NNYLF Ta Gargaɗi Atiku Da Sowore Kan Cinna Wutar Rikici A Nijeriya

Ƙungiyar NNYLF Ta Gargaɗi Atiku Da Sowore Kan Cinna Wutar Rikici A Nijeriya

October 17, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Dalilin Karyewar Farashin Kayan Abinci

Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Dalilin Karyewar Farashin Kayan Abinci

October 17, 2025
Tinubu

Batun Yin Afuwa Ga ‘Yan Yankin Ogoni Huɗu

October 17, 2025
Shettima

‘Yan Nijeriya Na Dab Da Fita Daga Halin Kuncin Talauci – Shettima 

October 17, 2025
Manzon Allah

Manzon Allah (SAW) Ne Ya Kafa Tushen Wayewar Kai A Duniya

October 17, 2025
An Kashe Mutane Da Dama Da Kone Gidajensu A Wani Hari Da Aka Kai Benuwai

Yadda ‘Yan Bindiga Ke Zafafa Hare-hare A Jihohin Arewa Maso Yamma

October 17, 2025
Shugaban Najeriya Ya Kaddamar Da Aikin Samar Da Ruwa Da Kamfanin Sin Ya Gudanar A Birnin Abuja

Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka: Ta Bar Baya Da Ƙura

October 17, 2025
Tsohon Ɗan Majalisar Bayelsa Ya Shawarci Jonathan Ya Guji Neman Takara A 2027

Tsohon Ɗan Majalisar Bayelsa Ya Shawarci Jonathan Ya Guji Neman Takara A 2027

October 17, 2025
Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

October 16, 2025
NAWIA

Ranar Abinci Ta Duniya: NAWIA Ta Tallafawa Mata 114  Da Kayan Aikin Gona A Zamfara

October 16, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.