Babban Jami’in Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya, Mista Matthias Schmale, ya bayyana cewa kudirin da ya sa aka kafa Maja;lisar Dinkin Duniya na fuskantar kalubalen da ba a taba ganin irinsa ba saboda yadda yaki ke ci gaba da gudana a sassan duniya.
Ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi game da ranar Majalisar Dinkin Duniya, wanda ake gudanarwa kowace shekara don tunawa da muhimmiyar ranar da Yarjejeniyar Kafa Majalisar Dinkin Duniya ta fara aiki, 24 ga Oktoba,1945.
A jawabin nasa wanda Jami’ar yada labarai bangaren Hausa na Ofishin Bayar da Bayanai na MDD da ke Abuja, Maryam Rabi’u ta raba wa manema labarai a yau Talata, babban jami’in ya yi tsokaci a kan ka’idoji da ayyukan Majalisar Dinkin Duniya da kuma kalubalen da duniya ke fuskanta a yau.
Mr. Schmale ya fara ne da tabo batun yadda aka bude taron Yarjejeniyar Kafa Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya jaddada cewa babban kudirin kafa hukumar shi ne “ceto al’ummar duniya daga bala’in yaki.”
A bikin na bana, ya bayyana cewa, wannan kudiri na fuskantar kalubalen da ba a taba ganin irinsa ba, inda tashe-tashen hankula suka shafi miliyoyin mutane a wurare kamar Ukraine, Falasdinu, Isra’ila, Sudan da Myanmar, da kuma korar shugaban Nijar da aka yi a kwanan baya.
- Nijeriya Ta Yi Nasara A Kotun Ingila Kan Rikicinta Da Kamfanin P&ID
- An Kwato Bindiga AK47 Guda 150 A Minna Bayan Artabu
Babban Jami’in ya bukaci kasashen kungiyar su sake jaddada sadaukarwarsu da girmama Yarjejeniyar ta Majalisar Dinkin Duniya, da kuma sabunta kokarinsu na inganta zaman lafiya, yana mai bayyana cewa, wannan shi ne muhimmin sakon Babban Sakataren MDD Antonio Guterres a bana.
Ya kuma yaba wa ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya a Nijeriya, wadanda suke aiki ba tare da gajiya ba, a lokuta da dama a cikin mawuyacin hali, domin cika burin Majalisar Dinkin Duniya na samar da zaman lafiya da wadata ga kowa da kowa.
Ya kuma tuna tare da bayyana alhini kan ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya guda 23 da suka rasa rayukansu a harin ta’addancin da aka kai a ofishin MDD da ke Abuja a shekarar 2011 da kuma abokan aikinsu da ke ci gaba da sadaukarwa a yanayi na tashe-tashen hankula.
Mr. Schmale ya kuma bayyana kudira MDD kan cimma ajandar 2030 da kuma manufofin ci gaban zamani masu dorewa (SDGs), tare da jaddada ka’idar kowa ya bayar da gudunmawa a dama da shi ba tare da barin kowa a baya ba. Ya yi alkawarin mayar da hankali wajen magance matsalolin da suka shafi yara da ba su zuwa makaranta, rashin abinci mai gina jiki, cin zarafin mata da ‘yan mata, da bukatun al’umma masu rauni da suka hada da tsofaffi, nakasassu, da ‘yan gudun hijira.
Har ila yau, ya yi kira ga shugabannin gwamnati da su hanzarta aiwatar da ajandar 2030 sannan ya yi magana game da dimbin damar da Nijeriya ke da ita ta bunkasa da ciyar da kanta gaba, yana mai jaddada bukatar mayar da hankali wajen aiwatar da lamarin bilhakki.
Taken bikin ranar Majalisar Dinkin Duniya na bana, “Hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya tare da Nijeriya don Cimma Tsarin SDGs,” ya mayar da hankali ne a kan bayyana mahimmancin haɗin gwiwa da sauke nauyin da ke wuyar juna.
Babban Jami’in ya jaddada kokarin da majalisar ke yi na kara samun kayan aiki don magance matsalolin kiwon lafiya kamar cuta mai karya garkuwar jiki (AIDS), da tarin fuka, da zazzabin cizon sauro, da kuma tallafa wa samar da zaman lafiya, magance rikice-rikice, da inganta hanyoyin sa ido ga rundunar ‘yan sandan Nijeriya.
Bugu da kari, ya amince da ayyukan jin kai a jihohin Borno, Adamawa, da Yobe, inda aka bayar da agajin gaggawa ga marasa galihu miliyan 3.6 a farkon rabin shekarar nan.
Mr. Schmale ya kuma tunatar da kowa da kowa cewa dole ne dukkanin ayyukan ci gaba su kasance daga tushe a cikin mutunta hakkin Dan’adam, bayar da shawarar ‘yancin fadin albarkacin baki, da kuma dakile kalaman batanci da kiyayya.
Mr Schmale ya kammala jawabinsa da neman hadin kai da hadin gwiwa tsakanin gwamnati, kungiyoyin fararen hula, bangarori masu zaman kansu, da kafafen yada labarai wajen tabbatar da akidu da ganin kimar Majalisar Dinkin Duniya don ci gaban mutanen duniya da samun wadata, da zaman lafiya.